• English
  • Business News
Friday, September 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Nijeriya 376 Aka Kwaso Daga Sudan – Minista Sadiya

Ba za mu bar ko mutum ɗaya a ƙasar ba, inji ta

by Sulaiman
2 years ago
in Labarai
0
‘Yan Nijeriya 376 Aka Kwaso Daga Sudan – Minista Sadiya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jimillar ‘yan Nijeriya 376 da su ka maƙale a ƙasar Sudan sun iso Abuja lafiya sakamakon aikin kwaso su da Gwamnatin Tarayya ke yi. 

Mai ba da shawara ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Miss Nneka Anibeze, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta ba manema labarai a ranar Alhamis.

  • Shekara 61 Da Haihuwar Sam Nda-Isaiah: Waiwayen Mukarrabai Kan Mashahuran Hikimominsa

Ta ƙara da cewa kashin farko na mutanen da aka kwaso, wato mutum 94, sun sauka ne a daren ranar Laraba a jirgin Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya samfurin Hercules C-130, yayin da sauran mutum 282 su ka sauka a jirgin kamfanin Air Peace.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta tsaya a filin jirgin sama na Abuja domin tarbar waɗanda aka ceto daga Sudan ɗin.

A jawabin maraba da ta yi masu, ministar ta yi godiya ga Gwamnatin Tarayya saboda tattaunawar fahimtar juna da ta yi da gwamnatin Sudan wadda har ta kai ga samun karɓar ‘yan Nijeriya tare da kwaso su daga ƙasar da yaƙi ya ɓarke.

Minista Sadiya

Ta ce: “Mun yi murna da ganin sun iso lafiya kuma babu wani rai da ya salwanta. Sun sha matuƙar wahala amma mun gode wa Allah da su ka iso gida lafiya.

“Mu na gode wa Gwamnatin Tarayya saboda nasarar da aka samu a aikin ceto ‘yan Nijeriyar da ke Sudan. Mu na addu’ar a samu zaman lafiya a Sudan da ma kowane ɓangare na ƙasar nan.

“Yaƙi ba abu ne mai kyau ba. Kun dai ga yadda mutanen da su ka tafi karatu su ka zama ‘yan gudun hijira ba zato ba tsammani. Wannan ba kawai bala’i ne na ƙasa da ƙasa ba, a’a, bala’i ne kuma da ya shafi jinƙan rayuwar bil’adama.

“Za mu ba ko wannen su kuɗi N100,000 domin su yi kuɗin mota zuwa wajen iyalan su. Haka kuma mun tanadar da masauki a otal ga waɗanda aka kwaso ɗin har sai sun haɗu da iyalan su, yayin da kuma waɗanda ke buƙatar a duba lafiyar su an yi masu hakan.“

Minista Sadiya kuma ta bayyana cewa kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya umarta, babu wani ɗan Nijeriya da ke son ya tsere daga halin da ake ciki a Sudan da za a bar shi a baya.

Ta ce, “Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa da kuma Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje da sauran ma’aikatun gwamnati irin su NEMA, NCFRMI, NIDCOM, NIA da Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya su na aiki tare da Ofisoshin Jakadancin Nijeriya da ke Sudan, Masar, Etofiya da Chadi domin tabbatar da cewa ko mutum ɗaya ba a baro ba. Don haka, dukkan ɗan Nijeriyar da ke so ya tsere daga halin da ake ciki a Sudan za a dawo da shi gida cikin tsaro da darajtawa.

“Aikin kwashe mutanen ya gudana ne ta hanyoyi masu wuyar sha’ani na wasu mutane da su ka zama dillalai a lamarin, wanda hakan ne ya sa aka riƙa fuskantar matsalolin da aikin ya ci karo da su. An shirya ci gaba da kwaso mutanen mu kuma aikin zai gudana da sauri-sauri fiye da da har sai an kwashe dukkan ‘yan Nijeriya da ke Sudan an kawo su gida.”

Ita dai Sudan, ta auka cikin rikicin yaƙi ne a ranar 15 ga Afrilu lokacin da wasu sassa na sojojin ƙasar masu adawa da juna su ka fara kai wa juna hari a birnin Khartoum da yankin Darfur.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Batun Daurarru 3,298 Masu Jiran Hukuncin Kisa A Nijeriya

Next Post

A Nijeriya Ake Sarrafa Taliyar Indomie, Ana iya Amfani Da Ita Ba Matsala – Shugabar NAFDAC

Related

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya
Labarai

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

1 hour ago
Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido
Manyan Labarai

Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

1 hour ago
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

3 hours ago
Gwamnan Abba Ya Gabatar Da Ƙudurin Haramta Auran Jinsi A Kano
Manyan Labarai

Gwamnan Abba Ya Gabatar Da Ƙudurin Haramta Auran Jinsi A Kano

6 hours ago
Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata
Labarai

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata

6 hours ago
Ahlul Faidhati Mai Diwani Group
Rahotonni

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

7 hours ago
Next Post
A Nijeriya Ake Sarrafa Taliyar Indomie, Ana iya Amfani Da Ita Ba Matsala – Shugabar NAFDAC

A Nijeriya Ake Sarrafa Taliyar Indomie, Ana iya Amfani Da Ita Ba Matsala – Shugabar NAFDAC

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

September 12, 2025
Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

September 12, 2025
Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

September 12, 2025
Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

September 12, 2025
Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

September 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

September 12, 2025
Kasar Sin Daya Ce Daga Cikin Kasashen Duniya Da Aka Amince Da Su a Matsayin Mafi Zaman Lafya

Kasar Sin Daya Ce Daga Cikin Kasashen Duniya Da Aka Amince Da Su a Matsayin Mafi Zaman Lafya

September 12, 2025
Gwamnan Abba Ya Gabatar Da Ƙudurin Haramta Auran Jinsi A Kano

Gwamnan Abba Ya Gabatar Da Ƙudurin Haramta Auran Jinsi A Kano

September 12, 2025
Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata

September 12, 2025
Ahlul Faidhati Mai Diwani Group

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

September 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.