Bayanan da suke fitowa a jiya Juma’a shi ne zababben shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jam’iyyar APC sun kawo karshen tataburzar neman jagororin majalisar kasa ta 10 da za a kaddamar nan da ‘yan kwanaki.
Jaridar LEADERSHIP ta gano cewa Tinubu da gwamnonin daga karshe sun tsayar da tsohon ministan kula da harkokin Niger Delta, Sanata Godswill Akpabio (Dan shiyyar Kudu Maso Kudu), a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa da za a kaddamar nan kusa kadan.
Kazalika, sun kuma zabi Sanata Barau Jubrin, da ke wakiltar mazabar Kano ta Arewa (Da ya fito daga shiyyar Arewa Maso Yamma) a matsayin mataimakin shugaban majalisardattawa ta 10.
Majiyoyi sun shaida ma wannan jaridar cewa, Tinubu ya kuma tsayar da Tajudden Abbass, dan majalisa da ke wakiltar mazabar Zariya daga jihar Kaduna (Dan shiyyar Arewa Maso Yamma) a matsayin Kakakin majalisar wakilai ta 10.
Sannan, mataimakin kakakin majalisar wakilai kuwa an bai wa Benjamin Kalu, da ke wakiltar mazabar Bende a jihar Abia.
Tsarin rabon mukaman majalisa ta 10 din ya kai ga fitowa ne a wani zaman da jiga-jigai 8 na jam’iyyar APC suka yi a Abuja jiya.
Ganawar wacce ta gudana a karkashin jagorancin Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu; sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore; mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa, Sanata Abubakar Kyari da mataimakin shugaban APC na shiyyar Kudu, sannan Chief Emma Eneukwu shi ma ya halarci zaman.
Har-lau, shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Sanata Ahmad Lawan; mataimakinsa, Sanata Ovie Omo-Agege da kakakin majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila duk sun halarci ganawar.
LEADERSHIP ta gano cewa ya kamata a ce zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ma ya halarci zaman amma bai samu zuwa ba.
Cikin kwarin guiwa wani makusancin Tinubu a tawagar yakin neman zabensa, ya shaida ma wakilinmu cewa zaman ya gudana ne a gidan Tinubu da ke Abuja jiya.
Tinubu a makon jiya ya kafa kwamitin mutum 9 da su zauna su tsara yadda za a kasafta jagorancin majalisar kasa zuwa shiyya-shiyya yadda ya dace.
Majiyoyi masu karfi a wajen zaman sun shaida ma wannan jaridar cewa zabin Sanata Akpabio ya gamu da zafafan muhawara da tirjiya, inda Sanata Ahmed Lawan ya nuna adawarsa bisa wanda aka zaba da cewa shi ne zai gajeshi.
A makon jiya ne dai Lawan ya jagoranci tawagar wasu Sanatoci zuwa ga Tinubu inda suka yi shuri da kokarin zabin Akpabio, inda suka tsaya-kai-da-fata cewa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom din bai cancanci zama kan wannan kujerar ba.
Kuma duk da hakan, Tinubun ya sanya kafa ya shure hakan tare da daukan matsayar cewa Akpabio shi ne sabon shugaban majalisar dattawa ta 10.
Majiyoyinmu da basu bukaci mu bayyana sunansu ba, sun kara da cewa, zabin kakakin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa daga shiyya daya ta Arewa Maso Yamma shi ma ya janyo daga jijiyar wuya a wajen zaman.
An tattaro cewa wasu daga cikin wadanda suka halarci zaman sun yi boren cewa bai dace da siyasa ba kuma ba kama hankali ba a cewa manyan mukaman biyu sun fito kawai daga shiyya daya na arewa maso yamma.
Sun nuna damuwarsu gaya kan yadda ake kokarin maida shiyyar arewa ta tsakiya saniyar ware wajen rabon mukamai a majalisar.
Sun kuma tunasar da zaman cewa, shiyyar arewa ta tsakiya ta zabi APC sosai a zaben da ya gudana.
Majiyoyinmu suka ce, “Sanata Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da ke barin gado, ya nuna adawarsa da rashin amincewarsa da zabin Akpabio a matsayin wanda zai gaje shi, amma Tinubu ya tilasta masa yin shiru, hakan ya sa bai da zabi da ya wuce ya ja bakinsa ya yi gum.”
“Su ma wadanda suka yi adawa da zabin kakakin majalisa da mataimakin shugaban majalisar dattawa daga shiyyar arewa maso yamma sun yi tsit baya ganin yadda aka dosa. Mun shiga kai cikin wani yanayi ta yadda aka kwashe mukamai biyu aka tura zuwa shiyya guda daya. An yi watsi da shiyyar arewa ta tsakiya wajen rabon mukaman amma duk da ankararwar da aka yi karfin ikon zababben shugaban kasa ya shafe ra’ayin kowa,” majiyoyinmu suka shaida mana.
Domin tabbatar da wannan zabin, tawagar yada labaran Tajudden Abbas sun fitar da sanarwar manema labarai a jiya suna masu nuna zabin da Tinubu ya yi wa kakakin majalisar ta dace sosai.
Sun nakalto cewa Abbas zai yi kokarin hada kai, kyautata shugabanci da yin aikin hadin guiwa da sashin zartaswa. Kana sun nuna cewa Abbas din ya cancanci rike wannan mukamin da kuma gogewa da saninsa a bangaren majalisa da zana doka.
Har-ila-yau, da akwai alamun da ke cewa duk da wannan matakin, masu neman kakakin majalisar wakilai za su cigaba da neman sa’arsu duk da matakin na Tinubu duk da tsarin rabon mukaman da Tinubu ya yi.
An gano cewa ‘yan majalisar da basu gamsu da wannan tsarin ba za su yi bore wa Tinubu da APC su cigaba da neman kujerar.
Bayanan da LEADERSHIP ta gano na nuni da cewa mataimakin kakakin majalisar wakilai mai barin gado, Idris Wase bai amince da janye muradinsa na neman shugabancin majalisar ta wakilai ba.
An gano cewa sun kira taron gaggawa na ganawa da magoya bayansu domin duba batun da neman hanyoyin da za su bullo wa zancen.
“Dukkaninsu biyu da Wase da Betara sun ki amincewa da tsarin rabon mukaman da APC ta yi. Da yiyuwar za su yi watsi da tsarin da APC ta yi su cigaba da neman mukamin.”