Zababben Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdul’Aziz Abubakar Yari, ya ki amincewa da rarrashin da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi masa na ya janye muradinsa na neman shugaban majalisar Dattawa ga Sanata Godswill Akpabio.
Ya ce shi kam zai cigaba da neman kujerar abunsa.
- Mirginawar Rumbun Basuka A Jihohin Kano Da Kaduna
- Jaridar Business Day Ta Karrama Gwamnan Gombe Kan Hidimta Wa Al’ummarsa
Yari, wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce, neman kujerar shugaban majalisar Dattawa na gudanuwa bisa tsarin da kundin tsarin mulkin kasa ya shimfida ba wai kawai tsari ko ra’ayin wani ba.
Ya ce, “Abun da zai faru a wannan ranar zai faru ne bisa kundin tsarin mulkin kasa ba wai tsarin wani daban ba.”
Tsohon dan majalisar wakilai, ya misalta neman kujerar a matsayin harka ce da ta shafi Sanatoci bisa dogara da kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da ya basu ikon za su zabi shugabanninsu da kansu da kansu ba wai tsarin da wani zai shimfida musu ba.
LEADERSHIP ta labarto cewa a daren ranar Juma’a ne dai kusoshin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu suka zabi tare da tsayar Akpabio a matsayin wanda zai dake kujerar shugaban majalisar Dattawa ta 10 kodayake matakin na cigaba da daukan hankali da janyo zafafan muhawara.