Rundunar ‘yan sandan Jihar Akwa Ibom a ranar Asabar din da ta gabata ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da aikata barna a kamfanin sadarwa, ta hanyar yin shigar injiniyoyin don satar batir na kamfanonin sadarwa a jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai a shelkwatar rundunar, Uyo, babban birnin jihar yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin, kwamishinan ‘yansandan jihar, Olatoye Durosinmi, ya ce an samu nasarar kwato wasu batura guda shida na ‘mast backup’ da wata mota kirar Toyota Camry da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.
Kwamishinan ‘yansandan, wanda ya ce an kama su ne a ranar 21 ga Maris, 2023, ta hannun rundunar ‘yan sandan Eagle Response Skuad, bayan samun sahihan bayanai, ya sanya sunayen wadanda ake zargin sun hada da Chinwe Nwabara, Bright Godswill da Chinedu Nweke.
A cewarsa, wadanda ake zargin wadanda suka yi basaja da injiniyoyi sun tuka mota kirar Toyota Camry mai launin toka mai lamba KJA 321 FS tare da sace kayan aikin da kudinsu ya haura Naira miliyan 1.6 kafin a kama su.
Durosinmi ya ce, “A ranar 21 ga Maris, 2023, da misalin karfe 5 na yamma, bisa wani ingantaccen rahoto da aka samu cewa ‘yan bindigar da suka yi basaja a matsayin injiniyoyi, sun tuka mota kirar Toyota Camry mai launin toka mai lamba KJA 321 FS, a kewayen Uyo, Abak, Oron da Okobo, sun lalata su tare da satar batir na baya-bayan nan na kamfanonin sadarwa da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.6, wani dogon bincike da jami’an Eagle Response Skuad na rundunar ‘yan sandan ya yi ya kai ga cafke wasu mutane uku da ake zargi da suka hada da Chinwe Nwabara, Bright Godswill da Chinedu Nweke.
Ya ce an kuma kama wasu mutum hudu da suka yi garkuwa da wani babban sakatare na jihar Ignatius Brown na Karamar Hukumar Abak tare da neman kudin fansa Naira miliyan 80.
Ya ce ’yan uwa saboda bacin rai ne suka tattara wasu kudade suka biya wadanda ake zargin amma jami’an ‘yansanda sun samu nasarar gano maboyar barayin, inda suka ceto wanda aka sace tare da cafke wasu da ake zargi.
Ya ce an samu nasarar kwato bindigar gida guda daya da bindigu na katako guda uku daga hannun wadanda ake zargin.
A halin da ake ciki, daya daga cikin wadanda ake zargin, Sunday Ekwere, ya amsa laifin karbar Naira 850,000 daga kudin fansa da suka karba.sabo