Akalla ‘yan gudun hijira 3 ne suka rasa rayukansu da raunata wasu sojoji 8 a wasu hare-haren da mayakan kungiyar IS suka kai a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
A kwanakin nan an ruwaito yadda ISWAP ta harba bindigun RPG wanda ya raunata wasu masu yi wa kasa hidima da fararen hula a wani samame da suka kai a yankin Talala na ISWAP a ranar Talata a karamar hukumar.
- ISWAP Ta Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinkai 3 Da Masu Tsaro 2 A Borno
- Mayakan Boko Haram 443 Sun Mika Wuya Yayin Da ISWAP Ta Kashe Musu Sama Da Mutum 300
Wani ma’aikacin Civilian Joint Task Force (CJTF) ya shaida wa wakilinmu cewa wadanda suka tsere sun kai rahoton yadda lamarin ya afku ga sojojin.
“Hudu daga cikinsu ‘Yan gudun hijirar sun je diban itace da safe amma abin takaici mutum daya ya dawo da raunukan harsashi. Mun gano gawarwaki uku daga tafkin, an harbe su a ka, kuma an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” inji majiyar.
Wata majiyar tsaro ta yi ikirarin cewa, a wani harin da sojoji suka kai, sun kashe mayakan ISWAP da ba a tantance adadinsu ba.
Akalla mutane 12 da suka hada da sojoji 8 da suka jikkata a lamarin, wanda ya faru a yankin Talala na ISWAP ranar Talata.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa da sanyin safiyar jiya ne wani jirgi mai saukar ungulu na sojoji ya zo Damboa domin kai wadanda suka jikkata zuwa Maiduguri domin yi musu magani.
Haka kuma, wani dan kungiyar ‘yan banga da ya shiga aikin ya shaida cewa mayakan na ISWAP sun harba bindigun RPG a wajen sojojin wanda ya yi sanadin salwantar rayuka.