ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisa Ta 10: Zababbun Sanatocin APC Na Arewa Ta Tsakiya Sun Yi Fatali Da Zabin APC

by Abubakar Abba
3 years ago
Majalisa

Zababbun Sanatocin da suka fito daga Arewa ta Tsakiya a karkashin jam’iyyu daban-daban, sun nuna rashin amincewa da mukaman shiyya da jam’iyyar APC ta sanar.

APC a shirin da ta yi, ta sahale wa Sanata Godswill Akpabio da ya fito daga shiyyar Kudu Maso Kudu ya zama shugaban majalisar dattawa a majalisar ta 10, inda kuma Sanata Barau Jibrin, daga Arewa Maso Yamma zai zama mataimakinsa.

  • Manyan Jami’an Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Game Da Alakar Kasashen Biyu
  • Wakilin Kasar Sin Zai Kai Ziyara Turai Dangane Da Samar Da Mafita Ga Rikicin Ukraine

Haka zalika, a majalisar wakilai kuwa APC ta sahalewaTajudeen Abass daga Arewa Maso Yamma da ya zama shugaban majalisar wakilai, inda Benjamin Kalu daga Kudu Maso Gabas zai zama mataimakinsa.

ADVERTISEMENT

Hakan ya tilasta wa zababbun Sanatocin da suka fito daga Arewa Maso Tsakiya rubuta wa shugaban APC na kasa Abdullahi Adamu wasika, inda suka sanar masa da kin lamunta da matsayin na APC ta kasa.

Sun bayyana cewa, a cikin wannan tsarin, ba a sanya Arewa ta Tsakiya a ciki ba duk da cewa zababben shugaban kasa da mataimakinsa, ba daga shiyyar suka fito ba.

LABARAI MASU NASABA

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Wasikar mai taken: matsayar da yan majalisa suka cimma kan shugabancin majalisa ta 10 kan shugabancin shiyya.

Sanatoci 18 ne suka rattaba hannu kan wasikar wadanda suka hada da, Sanata Mohammed Sani Musa daga Neja ta Gabas, Sanata Ashiru Oyelola Yisa daga Kwara ta Kudu, Sanata Sadik Umar Suleiman daga Kwara ta Arewa, Sanata Mustapha Saliu daga Kwara ta Tsakiya da kuma Sanata Isah Jibrin daga Kogi ta Gabas.

Sauran su ne, Sanata Abba Moro daga Benuwe ta Kudu, Sanata Godiya Akwashiki daga Nasarawa ta Arewa, Sanata Ahmed Aliyu Wadada daga Nasarawa ta Yamma, Sanata Ireti Kingibe daga Birnin Tarayya, Sanata Sunday Karimi Stebe daga Kogi ta Yamma, Sanata Sadiku Abubakar daga Kogi ta Tsakiya da kuma Sanata Peter Ndalikali Jiya daga Neja ta Kudu.

Har ila yau, sun kuma hada da Sanata Napoleon Binkap Bali daga Filato ta Kudu, Sanata Mwadkion Simon Dabou daga Filato ta Arewa, Sanata Diket Plang daga Filato ta Tsakiya, Sanata Mohammed O. Onawo daga Nasarawa ta Kudu, Sanata Emmanuel M. Udende daga Benuwe ta Gabas da kuma Sanata Titus Tartenger Zam daga Benuwe ta Yamma.

Wasikar ta ce, mu Sanatocin da muka fito daga Arewa ta Tsakiya mun gudanar da ganawa a ranar 8 ga watan Mayu 2023, inda a ganawar ne, muka cimma wannan matsaya, cewar shiyyarmu ta jima tana tabbatar da ci gaban siyasa a kasar nan kuma za ta ci gaba da yin hakan tare da ci gaba da goya wa zababben shugaban kasa baya.

A cewar wasikar shiyyar ta kuma samawar wa APC kuri’u kashi 41 a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabirairu, saboda haka, ita ma shiyyar lokaci ya yi da za a rama mata.

Bisa wadanan hujojin, muna kira ga APC ta kasa da ta gaggauta janye matsayar da ta cimma kan tsarin mukaman shugabancin majalisar ta 10.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola
Manyan Labarai

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa
Manyan Labarai

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
Next Post
An Cafke Wasu Mutane 2 Da Ake Zargi Da Kashe ‘Yan Sanda 3 A Delta

Yadda Likita Ya Yi Lalata Da Wata Mai Jinya A Asibitinsa A Jihar Kwara

LABARAI MASU NASABA

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025
Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.