Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wani magidanci mai suna Aminu Abubakar dan shekara 56 bisa laifin kashe matarsa.
Abubakar, mazaunin Lelewaji, Shagari Phase 2 a Yola, karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar, ya yi zargin ya yi wa matarsa Nana Fadimatu dukan tsiya har lahira, bayan ta fahimci shirinta na auren wani.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa
- Manyan Jami’an Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Game Da Alakar Kasashen Biyu
Ana zargin Abubakar da saki marigayiyar har sau biyu tare da ba ta masauki ba, har zuwa lokacin da ake sa ran za a sasanta auren. Amma kafin su sasanta, an ce marigayiyar tana shirin auren wani mutum, lamarin da ya fusata Abubakar, inda ya shiga tashin hankali.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRP) a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “Wanda ake zargin, Aminu Abubakar, mazaunin Lelewaji, Shagari Phase 2, a Karamar Hukumar Yola ta Kudu, ya yi wa marigayiya Nana Fadimatu dukan tsiya bayan wata ‘yar rashin jituwa da ta da ke tsakaninsu lokacin da ya ji labarin cewa marigayiyar za ta auri sabon miji wata rana.
Wanda ake zargin ya fusata ne inda ya kai ga danne ta a ranar 5/5/2023 da misalin karfe 10 na dare, ya buga mata wani abu mai karfi da hakan ya sa ta fadi sumamme, sannan daga baya aka sanar da cewa ta mutu.
“’Yansanda sun kama wanda ake zargin ne a shelkwatar ‘yan sanda ta Shagari sakamakon rahoton da aka samu daga sabon mijin da zai aure Mahmud Rufa’i na Shagari Anned, da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu.
“Ya zuwa yanzu dai, bincike ya nuna cewa wanda ake zargin shi ne manajan kamfanin ruwa na Anasam a gidan Jambutu 50 yana da da daya tare da marigayiyar bayan shekaru 9 da aurensu. “Kwamishanan ‘yan sanda CP Afolabi Babatola yayin da yake nuna kaduwarsa kan lamarin ya yaba wa DPO Shagari bisa kama wanda ake zargin ya kuma ce lallai za a gurfanar da shi gaban kotu domin hukunta shi.”
Ya kara da cewa CP din ya umurci jami’an sashen yaki da kashe-kashe masu alaka da CID na jihar da su dauki nauyin gudanar da bincike tare da tabbatar da doka ta yi aiki. Hakazalika ya yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton mutane masu aikata munanan laifuka ga ‘yan sanda.