Madam Amina J. Mohammed ita ce mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kuma shugabar kungiyar ci gaba mai dorewa ta Majalisar Dinkin Duniya.
Idan za a tunawa Amina Mohammed ta rike Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari kafin ta zama mataimakiyar sakatariyar majalisar UN a 2017.
- Yadda Likita Ya Yi Lalata Da Wata Mai Jinya A Asibitinsa A Jihar Kwara
- Manyan Jami’an Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Game Da Alakar Kasashen Biyu
Kafin nadin nata, Ms. Mohammed ta kasance ministar muhalli ta Tarayyar Nijeriya inda ta jagoranci kokarin kasar kan ayyukan sauyin yanayi da kokarin kare muhalli.
Ms. Mohammed ta fara shiga Majalisar Dinkin Duniya ne a shekarar 2012 a matsayin mai baiwa Ban Ki-moon tsohon babban sakataren Manofofin Ci Gaban Karni Na Majalisar Dinki Duniya (MDD) shawara Ta musamman da alhakin tsare-tsaren ci gaba bayan 2015.
Ta jagoranci tsarin da ya haifar da yarjejeniyar duniya ta shirin cigaba mai dorewa Nan da 2030.
Ms. Mohammed ta fara aikinta ne da aikin zayyana makarantu da asibitoci a Nijeriya. Ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta mayar da hankali kan inganta ilimi da sauran ayyukan zamantakewa, kafin ta shiga cikin ma’aikatun gwamnati, inda ta kai matsayin mai ba da shawara ga shugabannin hudu da suka biyo baya a kan talauci, gyara sassan gwamnati, da ci gaba mai dorewa.
An bai wa Ms. Mohammed digirin girmamawa da dama, kuma ta yi aiki a matsayin mataimakiyar farfesa, inda ta yi lacca kan ci gaban kasa da kasa. Wadda ta samu lambobin yabo daban-daban na duniya, Ms. Mohammed ta yi aiki a manyan kwamitocin ba da shawarwari na kasa da kasa. Tana da ‘ya’ya shida kuma tana da jikoki hudu.
MADOGARA (UN ORGANIZATION)
Haihuwa
An haifi Amina Jane Mohammed a Birnin Liberpool, dake Ingila a ranar 27 ga watan Yunin, 1961 mahaifinta likitan dabbobi ne da kuma mahaifiyarta malamar Jinya ce (nurse) Asalin ta Bafulatana ce daga Jihar Gombe Nijeriya.
Karatu
Amina ta halarci makarantar firamare a Kaduna da birnin Maiduguri a Nijeriya, sai kumaMakarantar “The Buchan School” da ke tsibirin Isle of Man.
Daga bisani ta halarci kwalejin Henley Management College dake birnin London a 1989. Bayan ta kammala karatun ta ne mahaifinta ya nemi ta da ta dawo gida Nijeriya.
Ayyuka
A tsakanin shekarun 1981 zuwa 1991, Amina tayi aiki da “Archcon Nigeria”, wani kamfanin zane-zane da suke da alaka da kamfanin zane-zane na Norman and Dawbarn da ke Ingila A 1991, ta samar da kamfanin Afri-Projects Consortium, sannan daga 1991 zuwa 2001 itace darekta mai zartarwa na kamfanin.
Daga shekara ta 2002 har zuwa shekara ta 2005, Amina ta shirya wani gangami da ilimantarwa game da jinsi karkashin United Nations Millennium Project. (Manufar manufar ita ce rage talauci, yunwa, cututtuka, jahilci, gurbacewar muhalli, da kuma cin zarafi tsakanin jinsi)
Amina ta rike matsayin mataimakiya ta musamman (Senior Special Assistant) na shugaban kasa akan shirin Millennium Debelopment Goals, Manofofin Cigaban Karni Na Majalisar Dinki Duniya (MDGs). A cikin shekara ta 2005, an zarge ta da amfani da kudin tallafi na kasa a wajen ayyukan MDGs.
Amina ta kasance wacce ta kafa kuma ta samar da kamfanin Center for Debelopment Policy Solution, sannan kuma a matsayin farfesa ta daliban masters a jami’ar Columbia.
A tsakanin wannan lokaci, tayi aiki a matsayin mai bada shawarwari na kungiyoyi daban daban na duniya wanda ya hada da, babban sakatariya a Majalisar Dinkin Duniya (UN) don zama na musamman akan Post-2015 “Debelopment Agenda”; da kuma Independent Edpert Adbisory Group.
Sannan har wayau ta rike matsayin chairman a Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya United Nations Educational, Scientific and Cultural Organization (UNESCO), da sashin bincike da bayanai akan ilimi na duniya “Global Monitoring Report on Education” (GME).
Har zuwa shekara ta 2012, Amina tana daya daga cikin muhimman mutane a taron e Post-2015 Debelopment Agenda, (Ajandar ci gaban bayan 2015 wani tsari ne daga 2012 zuwa 2015 wanda Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta don ayyana tsarin ci gaban duniya nan gaba wanda zai cimma nasarar muradun karni, Sabon tsarin, wanda ya fara daga 2016 ana kiransa Manufofin Ci Gaban Dorewa). inda take aiki a matsayin mai bada shawara na musamman ga shugaban majalisar dinkin duniya watau Ban Ki-moon, sannan tana daga cikin mutane na musamman na “High Lebel Panel of Eminent Persons (HLP)” da majalisar Open Working Group (OWG) da dai sauransu.
Daga shekara ta 2014, tayi aiki a matsayin babban sakatariya na “independent Edpert Adbisory Group on the Data Rebolution for Sustainable Debelopment.
Ministan Muhalli (2015-2017)
Amina tayi aiki a matsayin ministan muhalli a karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari daga watan Nuwamaban shekara ta 2015 zuwa watan Febrerun shekara ta 2017. A wannan lokaci itace wakiliyar Nijeriya a Kungiyar Kasashen Nahiyar Afurka wato “African Union (AU)” fannin kawo canji wanda Paul Kagame ke jagoranta.
Ta ajiye aikin Ministan muhalli a ranar 24 ga watan Febrerun 2017.
A cikin shekara ta 2017, wata kungiya mai zaman kanta ta zargi Amina da cewa tana ba da izini ga kamfanonin kasar China wajen diban itace timber zuwa kasashensu ba tare da izinin gwamnatin tarayya ba, a lokacin tana ministan muhalli na Nijeriya.
Amma daga bisani gwamnatin Nijeriya ta karyata zargin.
Mun samo daga Turakar Saliadeen a Dandalin Is’haki Idris Guibi