Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC), ya yi barazanar hukunta masu defo din mai masu zaman kansu da ke kin sayar da man fetur a kan farashin gwamnati.
Shugaban Kungiyar Dillalan Man fetur ta Kasa (IPMAN), Elder Chinedu Okoronkwo, ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis.
- Kwankwaso Da Fayose Sun Ziyarci Wike A Fatakwal
- Hajjin Bana: Saudiya Ta Hana Amfani Da Gas Din Girki A Lokacin Aikin Hajji
Ya ce kamfanin NNPC ya yi wannan gargadi ne a wata ganawa da shugabannin IPMAN a ranar Laraba a Abuja.
A cewar Okoronkwo, NNPC ya yi barazanar dena bai wa masu defo din man fetur idan har su ka ki sayar wa a kan farashin gwamnati.
Ya kuma bayyana cewa NNPC, ya bai wa shugabannin bangaren kula da mai na kasa da wajen teku (NMDPRA) da su sanya ido a kan tabbatar da umarnin gwamnatin.
Ya ce tun da gwamnatin tarayya ba ta kara farashin man fetur ba, to babu hujjar da masu defo masu zaman kansu za su kara farashin mai, inda ya jaddada cewa duk wanda ya kaucewa umarnin, zai fuskanci hukunci.