Wasu ‘yan bindiga sun kai wani hari inda suka kona ofishin ‘yan sanda da gidaje uku a kauyen Zugu na karamar hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara.
Sai dai wani shugaban matasa a Bukkuyum ya shaida wa manema labarai cewa babu wanda ya rasa ransa a sanadiyar harin kawo yanzu.
- Za Mu Hukunta Masu Defo Din Da Suka Ki Sayar Fetur A Kan Farashin Gwamnati — NNPC
- Kwankwaso Da Fayose Sun Ziyarci Wike A Fatakwal
Ya kara da cewa mazauna yankin sun tsere daga kauyukansu zuwa garin Bukkuyum da wasu kauyukan da ke cikin karamar hukumar Gummi mai makwabtaka domin neman mafaka daga hare-haren.
Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa kiran da manema labarai suka yi masa ba kan harin na kauyen Zugu.