A shirye-shiryen taron masu ruwa da tsaki da take shirin gudanarwa, Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) reshen Jihar Ribas, ta nemi a karfafa bunkasa kwazon bil’adama ga kwararrun ‘yan Nijeriya masu zaman kansu da ke aiki a bangaren tattalin arziki na Kamfanoni, Kungiyoyi don kawo ci gaban fasaha bisa tanadin gwamnati a tsarin tallafin da ‘yan kasashen waje da kamfanoni ke bayarwa.
Hukumar ta nemi a rika keɓe kaso na musamman don bai wa ɗaliban Nijeriya damar haɓaka ƙwarewar ɗan’adam a kan aiki don ba da damar samun nasarar koyon fasahar aiki kamar yadda aka tsara da kuma sanya su a cikin tanadin Tallafin Kirkiro da Fasaha. Inda hukumar ta NIS ta kara da cewa yawancin ƙwararrun ‘yan Nijeriya ba su samun damar haɓaka kwazon aiki cikin hikima da ɗaukar nauyinsu kamar yadda aka tsara.
Don haka, NIS reshen Jihar Ribas bisa jagorancin Kwanturola Sunday James, ta yunkura domin ganin alakar da ake da da kamfanoni a Jihar Ribas, ya kara zama mai muhimmanci domin ci gaban al’umma, da kawar da takaici da kuma guje wa tabarbarewar kwakwalwa sakamakon rashin gamsuwa da kwazon aiki da kawo wa bangaren sana’o’i ci gaba a cikin gida.
- NIS Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Zuba Jari A Nijeriya –CI James
- Ma’aikatar Hukumar Shige Da Fice Ta Nijeriya Na Gayyatar Jarabawar Daukar Aiki
Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Jihar Ribas, James Sunday, kamar yadda wata sanarwar manema labarai daga reshen hukumar ta nunar, yana da ra’ayin cewa ya kamata ’yan Nijeriya da suka cancanta su ci gajiyar aikinsu a cikin gida, ka da ya zama ‘yan kasar waje na amfani da su ne kawai sannan idan sun gama su tsere zuwa kasashensu na asali tare da barin ‘yan kasa da neman ayyuka masu gwabi a ketare.
A ganin Kwanturolan, ayyukan da ake bai wa ’yan Nijeriya sai ya zama dan kasar waje yake kula da su, idan dan kasar wajen ne ya fi saninsa, domin a samu damar koyar da ‘yan kasa fasahar wanda shi ne dalili na farko na sashen shirin dalibai a cikin tsarin Tallafin ‘Yan Kasar Waje da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta amince da shi kuma Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya ta aiwatar.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa reshen Jihar Ribas na karfafa gwiwar masana’antu, kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu na tattalin arzikin kasa da kuma sauran hukumomin bangaren gwamnati da su hada kai da Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya don bai wa ’yan Nijeriya ƙwararru damar kara inganta kwarewarsu ta sanin makamar aiki.
Ta kara da cewa, domin samar da kyakykyawan aiki na ilimi da samar da aikin yi, dole ne a yaki matsalar tabarbarewar kwakwalwa musamman ga kwararrun ‘yan Nijeriya da ke da aikin yi don karfafa ingantaccen ilimi da ilmantarwa maimakon ba da shaidar karatu kawai, “Shawarar hakan tana cikin shirye-shiryen taron wayar da kan masu ruwa da tsaki a jihar ta Ribas.” In ji NIS reshen jihar.