ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bai Kamata A Ba Emefiele Hutun Zuwa Karo Karatu Ba –Matawalle

by Sadiq
3 years ago
Matawalle

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kalubalanci matakin bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele dama ya tafi hutun karo karatu.

A cewar Matawalle, akwai bukatar Emefiele ya tsaya ya yi bayani game da “shirin samar da sabbin kudade mara kan-gado” da ya kirkiro, wanda ya jefa al’umar Nijeriya cikin mummunan yanayi.

  • Buhari Ya Yaba Wa Hilda Baci Kan Daukaka Nijeriya A Idon Duniya A Fannin Girke-Girke
  • Rikicin Sudan: Kashin Karshe Na ‘Yan Nijeriya Sun Iso Gida 

A makon da ya gabata rahotanni sun yi nuni da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sahalewa Emefiele tafiya hutun karo karatu a kasar waje.

ADVERTISEMENT

Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, gwamna Matawalle, ya nemi Buhari da ya soke hutun domin Emefiele na da tarin batutuwan da ya kamata ya yi bayani a kai ga sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ke shirin karbar mulki.

“Ina so na yi kira ga Shugaba Buhari, da kada ya amince da hutun zuwa karo karatu ga duk wani ma’aikaci da yake da muhimmiyar rawa da zai taka wajen ganin sabuwar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta fara aiki.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

“Daya daga cikin wadannan mutane da rahotannin kafafen yada labarai ke cewa sun nemi izinin tafiya hutun karo karatu shi ne, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele.”

Gwamnan na Zamfara ya kara da cewa, Shugaba Buhari da mai dakinsa suna da kyakkyawar niyyar ganin an mika mulki salim-alim, “amma akwai wasu jami’ai da ke neman su haifar da rudani wajen tabbatar da aukuwar hakan.”

Matawalle sunan Emefiele kadai ya kama, bai ambaci sauran jami’an ba.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka maka CBN a kotu wajen kalubalantar shirin sauya kudaden da aka yi.

Leadership Hausa ta ruwaito cewa fadar gwamnatin Nijeriya ta ce ba ta da masaniya kan shirin bai wa Emefiele hutun zuwa karo karatu.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi

Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.