Mukaddashin mataimakin shugaban Jami’ar Koyarwa ta Modibbo Adama da ke Yola (MAU), Farfesa Muhammad Musa Malgwi, ya rasu a ranar Alhamis.
Sanarwar da Jami’ar ta fitar, mai dauke da sa hannun rajiistara, Hajiya Halima Bala, ta ce mamacin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, lokacin da yake gudanar da aikin da Jami’ar ta tura shi Abuja.
- Matsalar Kasa Biyan Basusukan Da Amurka Take Fuskanta Za Ta Kawowa Duniya Asara
- EFCC Na Binciken Gwamnan Zamfara Kan Almundahanar Biliyan 70
Ta ce mamacin wanda kafin rasuwarsa shi ne makaddashin mataimakin shugaban Jami’ar, ya rasu ya bar matarsa Farfesa Anna M. Malgwi, da ‘ya’ya.
Ta kara da cewa baya ga kasancewar Farfesa Malgwi, mukaddashin mataimakin shugaban Jami’ar ya kuma rike mukamai da dama a Jami’ar da kasancewarsa shugaban tsangayar kimiyyar zamantakewa.
Sanarwar ta ce nan gaba, iyalan mamacin za su sanar da lokacin jana’izarsa.