A ‘yan kwanakin nan duniya na fuskantar rikice-rikice wanda da ya taso daga rikice-rikice nal’umma ne da suka jawaowa kansu da kansu.
Bayar darahotattannin abubuwan da kefaruwa a irin wanna lokaci na tashin hankali, aiki ne na dan jarida wanda sai ya fara sadaukarda rayuwarsa tun da farko kafin ya iya cimma wanna manufarba kawo wa duniya halin da ake ciki.
- Bani Da Wani Gida A Kasar Waje -Buhari
- Bai Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Bi Sahun Ta Buhari Ba —Shugaban EYN
Amma wannan ba ma shi ne babbar matsalar da dan jarida kefuskanta ba a yayin gudanar daaikinsa na bayar da labarin yaddaal’amurran ke gudana a fagagen fama, amma babbar matsalar ita ce samun ‘yancin gudanar da aikinsa na yada labarai.
Wannan ne babbar mastalarda ke a kan gaba a yayin da akebikin ranar ‘yancin ‘yan jaridata wannan shekarar ta 2023wanda ya gudana a ranar 5 gawatan Mayu.
Bukatar a bayyana wa al’umma cikakken yadda abubuwa ke gudana yana kara fitowa fili, a kan haka a ware wannan ranar don yin na zaritare da tattauna irin kasadar da ‘yan jarida ke dauka a yayin dasuke gudanar da ayyukansu dakuma bukatar kare ‘yancinsu afadin duniya yana kara fitowafili.
Rana ce ta nazari a kanmuhimmancin ‘yancin ‘Yan Jarida tare da lura dagudummawarsu ga tsarintabbatar da dimokradiyya da karrama wadanda suka rasa rayuwarsu a yayin da suke kokarin tabbatar da gaskiya atsakanin al’umma.
A daidai lokacin da duniya ke bukukuwan wannan ranar, yana da muhimmanci mu fahimci cewa, abubuwa da suka shafi kariya ga rayuwar ‘yan jarida da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki yana kara fuskantar barazana, wanda hakan yana kawo cikas ga sauran hakokkin bil ’adam. Domin yaki dawadannan manyan matsalolinya sanya a ka sa ‘yancin ‘yan jarida, kariya ga ‘yan jarida da kuma bukatar samar da ‘yancin samun bayanai a yayin gudanar da ayyuka ya zama a kan gaba abikin wannan shekarar.
‘Yancin fadin albarkacin bakin dan adam kamar yadda yake adoka ta 19 ta dokar kasa da kasata majalisar dinkin duniya yanada matukar muhimmanci kuma shi ne ke tabbatar da ‘yancin dan adam gaba daya.
A Nijeriya, bangaren yada labarai na fsukantar mastalata musamman wanda ke haifar da mastala ta yadda dan jarida ba zai iya gudanar da aikinsa ba cikin ‘yanci kuma ba tare datsoro ba.
‘Yan jarida a Nijeriya na fuskantar matsalolin da suka hada da barazana, cin mutunci da hare-hare musamman in suna bayar da rohoto a kan abubuwan da suka shafi muhimman lamari kamar su al’mundahana, cin zarafin bil adam, da matsalolin da suka shafi tsaro.
A lokutta dadama a kan kama dan jaridar akulle shi a kuma azabtar da shi akan suna gudanar da ayyukansu.
Barazanar da ake yi wa ‘yan jarida musamman daga ‘yansandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro wani babbar barazana ne.
Wannan babbar barazana ce ga ‘yancin yada labarai kuma baraza ne ce ta musamman ga tsarin dimokradiyya.
‘Yan jarida na da hakkin bayar da rahottanin da suka shafi rayuwar al’umma ba tare da an kai musu hari ba ko takura ba.
Katsalanda daga jami’an tsaroda mahunta ba abin a amince bane, dole a yi dukkan kokarin ganinan tabbatar da kariya da jami’an watsa labarai in ana son tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida.
Bayan wadanna matsalolin, bangaren watsa labarai a Nijeriya na fuskantar matsalolin tattalin arziki, a halin yanzu da yawa daga cikinsu na fuskantar cikasa yayin gudanar da ayyukansu a sassan kasar nan.
Wannan kuma ya haifar da rashin samun ingantaciyyar yanayin gudanar da aikin jarida, gidajen jarida da dama basa iya biyan albashin ‘yan jarida, basa kuma samun daman samun karin karatu ta yadda za su inganta kwarewar ayyukansu.
Akwai tsnananin bukatar ‘yan jarida su rungumi dokoki da ka’dojin aikin jarida a yayin gudanar da akinsu, kamar abin daya hada da tabbatar da labari kafin bugawa su kuma gujewa labarai masu tayar da hankali su kuma mutunta sirrin al’umma tare da kaucewa labaran kanzon kurege.
Duk da wadannan matsaloli a ra’ayinmu ya kamata ‘yan jarida su ci gaba da fadin gaskiya ga mahunkuta da kare hakokin al’umma ko da kuwa suna fuskantar barazana.
A daida lokacin da duniya ke kira ga samun ‘yancin ‘yan jarida, yana muhimmanci a tunatar da‘yan jarida a kan bukatar su kula da kansu, su rika daukar mataki na kariya a gare su kuma nemi kariyar doka a duk lokacin dawani abu ya taso a yayin gudanar da ayyukansu.
A ra’ayinmu kuma akwai bukatar jami’an tsaro su rungumi akidar kare ‘yan jarida kamar yadda tsarin mulki ya tanada.