Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya karyata rahoton da wasu kafafen yada labarai suka wallafa cewa, ya ce jami’in tsaro na gujewa ‘yan bindiga, amma suna cin zarafin mutanen da ‘yan bindigar suka sace.
Sultan din na Sakkwato kuma shugaban majalisar koli ta harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), ya karyata rahoton ne, a cikin sanarwar da babban sakataren cibiyar hulda da mabiya addinai ta kasa (NIREC) Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua, ya fitar a madadin Sultan.
Sultan wanda na daya daga cikin shugabanin NIREC sanarwar ta ce, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, bai furta cewa jami’in tsaro na gujewa ‘yan bindiga, amma suna cin zarafin mutanen da ‘yan bindigar suka sace ba.
Sanarwar dai, na mayar da martani ne dangane da jawabin da Sultan ya yi a ganawa ta kwana uku ta zango na biyu na 2023 da ya gudana a dakin taro na otel din NICON da ke Abuja.
Taken taron shi ne: Gudunmawar da kafafen yada labarai za su bayar don samar da inganccen shugabancin gina kasa.
Sanarwar ta kara da cewa, bayanin da Sultan ya yi a wajen taron, wasu kafafen yada labarai da aka gayyata daukar rahoton taron, ba su wallafa bayanin na Sultan daidai ba.
A cewar sanarwar, bayanin da Sultan ya yi a wajen taron shi ne, idan ‘yan bindiga suka kai hari cikin al’umma suka kashe mutane tare da kone gidaje, ba daukar wani mataki akai, inda bayan ‘yan bindigar sun kammala aikata ta’asar, sai jami’in tsaron su je inda abin ya auku, zuwan na su, me za su yi? sai dai kawai su iske tokar gidajen da ‘yan bindigar suka kone.”