An gurfanar da tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Ogun, Oludare Kadiri a gaban wata kotun majistare da ke Abeokuta bisa zargin barazana ga rayuwa da kuma tada zaune-tsaye.
Hakan dai ya biyo bayan wani sabani da aka samu yi a ranar Talata a zauren majalisar yayin da Kadiri ya toshe babbar kofar shiga harabar majalisar.
- Kwana 5 Ga Rantsuwa: Waiwaye Kan Rawar Da Matan Shugabannin Kasa Suka Taka A Baya
- Tony Blair Ya Ziyarci Tinubu A Abuja
An kama Kadiri, mai shekaru 54, daga baya kuma aka tuhume shi da laifuka biyu na barazana ga rayuwa da kuma haddasa rashin zaman lafiya.
Sai dai ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Watanni uku da suka gabata shi da magoya bayansa sun mamaye Majalisar don “tabbatar da” hukuncin soke dakatarwar da majalisar ta yi masa.
A watan Satumba, 2022 ne majalisar ta dakatar da dan majalisar da wani mutum bisa zargin tauye hakki na majalisar dokokin jihar.
An kuma tsige Kadiri a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
Sai dai wata babbar kotun Jihar Ogun da ta zauna a Abeokuta a watan Maris ta soke dakatarwar da aka yi wa Kadiri tare da sauran.
A ranar Talatar da ta gabata ne aka yi zargin cewa ya rufe babbar kofar harabar majalisar inda ya dage cewa dole ne a bar shi ya ci gaba da zama dan majalisar dokokin jihar domin ya ci gaba da gudanar da aikinsa kamar yadda kotu ta umarce shi.
An ga jami’an tsaro suna lallashin dan majalisar tare da shiga tsakani.
An dai ga tsohon mataimakin kakakin ne zaune a cikin motarsa yana latsa wayarsa, yayin da lamarin ya ci tura.
Dan sanda mai gabatar da kara, Lawrence Olu-Balogun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Maris da misalin karfe 8:40 na safe a harabar majalisar da ke Oke-Mosan.
Olu-Balogun ya ce wanda ake kara ya shiga harabar majalisar inda ya yi barazana ga rayuwar ‘yan majalisar da sauran jami’an da ke ciki.
Ya kuma kara da cewa wanda ake tuhumar ya kuma yi amfani da motarsa wajen tare kofar shiga majalisar.
Lauyan mai shigar da karar ya ce tsohon dan majalisar ya gudanar da kansa ne ta hanyar da za ta iya haifar da kawo matsala ga zaman lafiya ta hanyar kai hari wanda ya kawo cikas ga tsarin samar da doka a majalisar.
Olu-Balogun ya bayyana cewa an dakatar da wanda ake tuhuma tun watan Maris din 2022, amma ya yi ikirarin cewa ya samu hukunci daga wata babbar kotu a Ogun, inda ya nemi ya koma ofishinsa.
Ya kara da cewa a lokacin da wanda ake kara ya isa zauren majalisar, jami’an tsaron da ke kofar majalisar sun hana shi shiga harabar.
A cewar masa, laifukan sun ci karo da sashe na 86(1) da 249(D) na kundin laifuffuka na Ogun na shekarar 2006.
Babban alkalin kotun, Misis M.O. Osinbajo, ta ba da belinsa.
Alkalin kotun ta dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 1 ga watan Yuni.