Yayin da ya rage kwanaki kalilan a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban Nijeriya, wasu mashahuran ‘yan jarida da ke farauto labarai a fadar shugaban kasa, sun yi waiwaye adon tafiya a kan yadda ake tafiyar da harkokin mika mulki.
Har ila yau, domin fayyace abubuwan da suke faruwa a wajen bikin mika mulkin, ciki har da halartar manyan baki da kuma jawabai na tunawa da sabon shugaban da aka rantsar, ’yan jaridar, wadanda aka fi sani da wakilan gidan gwamnati, sun yi wa LEADERSHIP Hausa karin bayani kan abubuwan da za su kayatar a wajen bikin rantsuwar.
Wani babban da jarida mai suna Chesa Chesa, wadda ke daukar rahoto a fadar gwamnati tun a shekarar 2008, ya ce dama an saba, duk lokacin da za a mika mulki ga sabuwar gwamnati akan shirya gudanar da abubuwa da dama.
A cewarsa, an mai da hankali sosai kan jawabin shugaban kasa mai jiran gado, inda da yawa ke jiran su ji sanarwa ko yanke shawara da za su nuna alkiblar sabuwar gwamnati.
Ya ce jama’a, wadanda aka gayyata da wadanda ba a gayyace su ba, sun yi cincirindo a dandalin Eagle Skuare, wanda ‘yan sanda suka yi wa tsinke. Yanayin yawanci kamar biki ne. Har ma a wajen dandalin Eagle Skuare inda ake rera wakoki ga sunan sabon shugaban kasa da jam’iyyarsa ta hayar kida.
“Ana kewaye filin rantsar da shugaban kasa da jami’an tsaro. Sannan mutane kan yi kasuwanci daga nesa da harabar filin.
“Akan mai da hankali sosai kan shugaban kasa, kuma ba a kan mataimakin shugaban kasa ba. A ko da yaushe akwai shugabannin da ke kawo ziyara, musamman shugabannin Afirka. Yana daya daga cikin lokutan da sojoji da jami’an tsaro ke yin, fareti.
“Yawanci a kan yi raye-raye masu ban sha’awa da wasan kwaikwayo, wadanda ke nuna manyan kabilun kasa. Tabbas, baki, musamman masu manya-manya kan halarci taron cikin shiga ta alfarma.
“Abin sha’awa shi ne, za a ga shugaba mai barin gado tare da rakiyar matarsa. Bayan rantsar da sabon shugaban da mataimakinsa, shugaban da mataimakinsa mai barin gado sukan bar sashen manyan baki. Dukka bikin yana daukar kimanin sa’o’i uku ne ko fiye da haka,” in ji Chesa.
Wani babban da jarida, Sunday Ode, wanda bai wuce shekaru 13 ba a matsayin wakilin gidan gwamnati ya tafka muhawara a kan kudirin shugaban kasa, ya tuno jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, inda ya ce shi na kowa ne, sannan ba kowa ba.
Ode wanda ya yi tsokaci kan bikin rantsar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo karo na biyu, da kuma bikin rantsar da Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, Goodluck Jonathan da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce, “Kamar ‘yan siyasa, yawanci yana daya daga cikin abubuwan da ‘yan jarida ke sa rai tare da kyakkyawan fata dangane da batun fayyace bayanai da kuma alkawuran da kowane sabon shugaban kasa zai yi.
“Kar ku manta Yar’Adua ya girgiza duniya lokacin da ya bayyana cewa zaben da ya haifar da shi bai inganta ba. Kuma kar ku manta Buhari ya ce “Ni na kowa ne, ba na kowa ba ne”.
“Faretin sojoji yawanci abin kallo ne a duk taron kaddamar da ko dai wadanda ke kasa a dandalin Eagle Skuare ko kuma wadanda ke kallo daga nesa”.
Ode ya ci gaba da cewa, babban lokacin da ake gudanar da duk wani nadin sarauta, musamman ma wanda ya kawo sabuwar gwamnati, shi ne lokacin da shugaban kasa mai barin gado ya sauka daga mukaminsa kamar yadda aka yi tsakanin Jonathan da Buhari.
A halin da ake ciki kuma, babban mai fafutukar kare hakkin bil’adama, kuma kwararre a fannin shari’a, Cif Olisa Agbakoba (SAN), a jiya ya ce rashin tabbas da aka samu a bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai sa taron ya zama abin tunawa.
Agbakoba, babban jigo a fafutukar tabbatar da dimokuradiyyar kasa, ya jaddada cewa kararrakin da ake jira ba zai iya dakatar da kaddamar da shirin mika mulki ba, inda ya kara da cewa ba zai iya tunawa akwai wani lokaci da aka gabatar da irin wadannan koke-koke na dakatar da bikin rantsuwa ba.
Ya ce, “Batun da ya fi muhimmanci kamar yadda nake gani, shi ne damuwar ko za a yi bikin rantsuwa. Ina ganin wannan shi ne batun da ya fi daukar hankali wanda zai sa bikin ya zama abin ban mamaki fiye da sauran.
“A gare ni da kaina, ta fuskar doka, wannan bikin ba za a iya hana shi gudana ba saboda abin da ya faru, cewa an shigar da kara a kotu don haka dole ne mu jira.
“Abin mamaki game da ni a ce an hana yin rantsuwa. Wannan shi ne abin mamaki a gare ni.
Shi ma da yake nasa jawabin, Sanata Femi Okurounmu ya ce bai kamata a ce rantsar da zababbun masu mukamai ya samu tasgaro ba.
Sai dai ya ce abin da ake sa rai daga shugaban kasa mai jiran gado shi ne zai magance matsalolin da ke addabar Nijeriya.
Ya ce, “Ba matsalolin da ‘yan Nijeriya ke son a magance su kadai ba, a’a, wasu matsalolin da shi da kansa ya yi a lokacin da yake karkashin Cif Obafemi Awolowo da Abraham Adesanya ya kwashe tsawon wadannan shekaru kafin ya koma APC. Ina fata har yanzu zai tuna da wadannan abubuwan kuma ya kula da su.
‘’Sauran abin da ake sa rai shi ne ya koma tsarin mulkin 1953. Wannan yana daya daga cikin fifikon farko. Kundin tsarin mulkin da muke aiki da shi a yanzu yaudara ne, almubazzaranci ne, yana da tsada, mulkin kama karya ne, ba dimokradiyya ba.
“Idan ya koma ga kundin tsarin mulki na 1953, tare da gyare-gyaren da ya kamata, abin da nake ji shi ne, mu koma ga Jihohi 12 na Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) da aka kirkira lokacin yana shugaban kasa na soja.”
A kan yadda hakan zai iya kasancewa, Okurounmu ya ce, ”Na ce ya koma wancan tsarin. Idan ya yarda ya koma tsarin, me ya sa hakan bai tabbata ba? Mun gudanar da jihohi 12 a karkashin Gowon; za mu iya komawa tsarin. Kuma mun gudanar da kundin tsarin mulki na 1953- shi ne abin da muka yi aiki daga 1960 zuwa 1966 kuma ya yi mana amfani sosai.