Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karrama marigayi Shugaban Kamfanin Jaridun LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, da babbar lambar karramawa ta kasa (OFR).
A shekarar da ta gabata mutane da yawa sun bayyana mamakinsu a lokacin da sunan Nda-Isaiah ya yi batan-dabo cikin jerin sunayen wadanda za a karrama da lambar yabon ta kasa, duk da irin gudunmawar da ya baiwa gwamnatin shugaba Buhari.
- LEADERSHIP Da CMG Sun Karfafa Dangantakar Aiki A Tsakaninsu
- Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance
Duk da haka, a yanzu shugaban kasar ya gyara wannan lamarin, tare da amincewa da hidimar mawallafin jaridar ya yi.
Abokai da kuma abokan aikin marigayi Nda-Isaiah, wanda ya rasu cikin a ranar 12 ga Disamba, 2021, bayan wata gajeriyar rashin lafiya, sun yi kira da kan ba marigayin wannan karramawar ta kasa a ranar cikar haihuwarsa 61 a farkon wannan shekarar.
Tasirinsa marigayin ya wuce aikin jarida, domin shi ma ya yi fice a fagen siyasa, kasancewar ya yi sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasar nan, kuma sananne a jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan jinkirin karramawa ya zama wata shaida kan irin gwagwarmayar Nda-Isaiah da kuma tasirinsa wurin hidimtawa al’umma da kawo ci gaba mai dorewa
Matakin da shugaban kasar ya dauka na ba da lambar yabo ta OFR bayan rasuwarsa, ya nuna irin gudunmawar da ya bayar ga Nijeriya tare da bayyana irin mutuntawar da ya samu a tsawon rayuwarsa.