• Leadership Hausa
Monday, October 2, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa 10 Da Zaku So Sani Cikin Jawabin Bankwana Da Buhari Ya Yi Wa ‘Yan Nijeriya

Na Gyara Nijeriya Fiye Da Yadda Na Same Ta A 2015 - Buhari

by Muhammad
4 months ago
in Manyan Labarai
0
Abubuwa 10 Da Zaku So Sani Cikin Jawabin Bankwana Da Buhari Ya Yi Wa ‘Yan Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi jawabinsa na bankwana ga ‘yan kasar a ranar Lahadi da safe.

Sashen Hausa na TRT Afirka, ya yi bitar jawabin da shugaba Buhari ya gabatar, inda a jawabin nasa kwana guda kafin ya mika mulkin kasar ga Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin.

  • Na Gyara Nijeriya Fiye Da Yadda Na Same Ta A 2015 – Buhari
  • Ganduje Zai Mika Wa Abba Gida-Gida Ragamar Mulkin Kano, Don Halartar Rantsar Da Tunibu

Shugaban ya yi bayani kan yadda tafiyar mulkinsa ta kasance da kuma wasu matakai da ya dauka a matsayinsa na shugaba.

Ga dai wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya yi bayani a kai:

Godiya ga ‘yan Nijeriya
Shugaban kasar ya yi godiya ga jama’ar kasar kan goyon bayan da suka ba shi inda ya bayyana cewa irin kwarin gwiwar da suka ba shi ya taimake shi wurin jagorantar kasar.

Labarai Masu Nasaba

Tinubu Ya Amince Da Biyan Ma’aikata Karin Albashin N35,000 Na Wucin Gadi

Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

Haka kuma shugaban ya yi godiya ga miliyoyin ‘yan kasar wadanda suka yi masa addu’a a lokacin da ya yi rashin lafiya a wa’adinsa na farko.

Taya murna ga Bola Tinubu
Shugaba Muhammadu Buhari ya kara taya murna ga zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu kan nasarar da ya samu ta cin zaben.

“Hakika ka yi aiki tukuru kan wannan rana kuma Allah ya biya maka bukatarka. Ba ni da shakka kan girma da kwarewa da adalci da sadaukarwa da nuna daidaito da biyayya da kake da ita ga kasa da kuma son da kake yi yi na Nijeriya ta samu ci gaba a idon duniya zai tabbata da ikon Allah, a lokacin da za ka jagoranci kasarmu zuwa matakin da ya fi wanda zan bar ta.

Haka kuma Shugaba Buharin ya bayyana cewa Tinubu ne dan takarar da ya fi cancanta.

Bayar da hakuri kan matakai masu tsauri
A jawabin nasa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya hakuri kan matakan da gwamnatinsa ta dauka masu tsauri amma ya ce matakan sun bayar da sakamako mai kyau.

“A yayin gyara tattalin arziki, mun dauki wasu matakai masu wahala, inda akasarinsu suka bayar da sakamako mai kyau.

Wasu daga cikin matakan sun kawo kunci da wahalhalu na wucin gadi kuma ina bayar da hakuri ga ‘yan kasata,” in ji Shugaba Buhari.

Amma ya bayyana cewa ya dauki matakan ne domin ci gaban kasar baki daya.

Kara inganta dimokuradiyya

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kara inganta dimokuradiyya a kasar domin kuwa zai bar tsarin zabe wanda yake tabbatar da cewa an kirga kuri’u kuma an samu sahihan kuri’u kuma an yi zaben gaskiya da adalci.

Shugaban kuma ya ce tsarin da ya bari ya kara rage tasirin kudi matuka a lokacin zabe wanda hakan zai sa jama’a su zabi wanda suke so.

Shugaban ya bayar da misali inda ya ce a zaben da ya gabata an ga wadanda ba su da kudi ko uban gida sun yi nasara kan sauran ‘yan takara masu kudi.

Taimaka wa talakawa
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wurin tallafa wa talakawa da mazauna karkara domin samun rayuwa mai kyau.

Ya bayyana cewa gwamnatinsu ta samar da abinci ga miliyoyin mutane da ke kauyuka da kuma bayar da dama ga mata domin su samu abinci.

“Matasa maza da mata da ke birane su ma mun taikama musu domin amfani da baiwarsu yadda ya kamata,” in ji shi.

Nasarori kan harkar tsaro
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi kokari wurin rage wasu daga cikin matsalolin da ake fama da su ne tsaro a kasar.

Shugaban ya ce sun samu sakamako mai kyau a yakin da suke yi na ganin cewa ‘yan Nijeriya na zaune lafiya.

“A yayin da nake kammala wa’adina, mun yi kokari wurin rage hare-haren ‘yan fashin da ‘yan ta’adda da fashi da makami da sauran laifuka,” in ji shugaban.

Haka kuma shugaban ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin ganin cewa ba a koma gidan jiya ba.

Kammala ayyuka
A yayin jawabin, shugaban ya tabo batun kokarin da gwamnatinsa ta yi wurin kammala ayyuka musamman ababen more rayuwa.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta kammala ayyukan da aka dade ba a kammala ba kamar wasu daga cikin ayyukan wutar lantarki da gadar Neja ta biyu da amincewa da sake fasali ga dokar man fetur da kammala muhimman hanyoyin da suka hade garuruwa da jihohin Nijeriya.

Jimamin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda aka sace
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu yana jimami kan yaran da ke tsare tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro na iyakar kokarinsu domin ceto su.

“Har yanzu ina jimami kan yaranmu da ke tsare, inda ta’aziyya ga iyaye da abokai da ‘yan uwan wadanda suka rasa masoyansu a lokutan da aka rinka kisa na rashin hankali.

Ga duka wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba, jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana domin ceto su cikin aminci,” in ji shi.

Yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban ya ce ‘yan Nijeriya suna sane da irin yadda zuciyarsu ke cike da burin ganin ya kawar da cin hanci da rashawa a kasar.

Ya bayyana cewa ya yi ta kokarin wannan yaki duk da irin turjiyar da ake samu.

“Na ji dadi ganin irin ci gaban da aka samu ta bangaren dawo da kudade masu yawa zuwa Nijeriya da kuma kwace kadarorin da aka saya da kudaden kasa,” in ji shugaban.

‘Nijeriya ta samu ci gaba fiye da 2015’
Batu na karshe da Shugaba Buhari ya yi a jawabin nasa na bankwana shi ne halin da zai bar kasar.

“Ina da yakinin cewa zan bar ofis a 2023 Nijeriya ta samu ci gaba fiye da 2015,” in ji shugaban.

A karshe shugaban ya yi godiya ga duka jama’ar kasar da kuma rokon Allah ya kara wa Nijeriya albarka.

Tags: BuhariJawabin Bankwana
ShareTweetSendShare
Previous Post

Buhari Ya Karrama Marigayi Sam Nda-isaiah Da Lambar Yabo Ta OFR

Next Post

Yadda Cutar Hawan Jini Ke Kisan Mummuke A Nijreriya

Related

Tinubu Ya Amince Da Biyan Ma’aikata Karin Albashin N35,000 Na Wucin Gadi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Amince Da Biyan Ma’aikata Karin Albashin N35,000 Na Wucin Gadi

15 mins ago
Mata
Manyan Labarai

Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

2 hours ago
BUA
Manyan Labarai

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 – Kamfanin

14 hours ago
Shekara 100 Da Kafa IAR: Da Sakamakon Bincikenmu Aka Kafa Ginshikin Tattalin Arzikin Arewacin Nijeriya —Farfesa Ishiyaku
Manyan Labarai

Shekara 100 Da Kafa IAR: Da Sakamakon Bincikenmu Aka Kafa Ginshikin Tattalin Arzikin Arewacin Nijeriya —Farfesa Ishiyaku

21 hours ago
Batun Yadda Samari Ke Barin Taimakon Iyaye Su Kashe Wa ‘Yan Mata Kudi
Madubin Rayuwa

Batun Yadda Samari Ke Barin Taimakon Iyaye Su Kashe Wa ‘Yan Mata Kudi

22 hours ago
Buhari
Manyan Labarai

Jawabin Shugaba Tinubu Kan Cikar Nijeriya Shekaru 63 Da Samun ‘Yancin Kai

1 day ago
Next Post
Yadda Cutar Hawan Jini Ke Kisan Mummuke A Nijreriya

Yadda Cutar Hawan Jini Ke Kisan Mummuke A Nijreriya

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Amince Da Biyan Ma’aikata Karin Albashin N35,000 Na Wucin Gadi

Tinubu Ya Amince Da Biyan Ma’aikata Karin Albashin N35,000 Na Wucin Gadi

October 2, 2023
Mata

Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

October 2, 2023
Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

October 1, 2023
Tinubu

Ranar ‘Yanci: Tinubu Ya Kara Wa Kananan Ma’aikata N25,000 Kan Albashinsu

October 1, 2023
Hangzhou

Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana

October 1, 2023
Syria

Shugaban Syria: Manyan Tsare-tsare Uku Na duniya Su Ne Jagororin Sabuwar Duniya

October 1, 2023
BUA

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 – Kamfanin

October 1, 2023
Kasar Sin

Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya Ya Shirya Bikin Murnar Cikar Sin Shekaru 74 Da Kafuwa

October 1, 2023
Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

October 1, 2023
Amurka

Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska

October 1, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.