‘Yan takara a jami’yyar PRP reshen jihar Kano karkashin kungiyarsu wacce Abdullahi Sabo Rano ke jagoranta, sun nemi sabuwar gwamnati jihar ta binciki tsohon gwamnan Jihar Umar Ganduje.
Sun sanar da wannan bukatar ne a wata ganawa da suka yi a makon da ya gabata a shalkwatar PRP da ke a jihar.
- Ra’ayoyin PDP, PRP Da SDP Kan Gudanar Da Zabe A Kano
- Muna Da Irin Akidar NEPU Da PRP A Siyasarmu -Shugaban SDP
Sun yi nuni da cewa, akwai mahimmanci sabuwar gwamnati ta yi waiwaye akan inda gwamnatin da ta gabata ta yi ba daidai ba da kuma inda ta yi daidai don a ciyar da Kano gaba.
Rano wanda ya bayyana hakan a madadin sauran ‘yan takarar, ya ce, akwai bukatar sabuwar gwamnatin ta yi dub kan yadda tsohuwar gwamnatin jihar ta kashe kudaden jihar, idan ta gano an yi sama da fadi da su, ta gudanar da bincike don a hukunta wadanda ke da hannu a aikata almundanar.
Ranon ya bayyana cewa, wajen da kuma gwamnatin ta baya ta yi kokari a gode mata a kuma dora akan ayyukan da ta faro don a ci gaba da bunkasa tattalin arzikin jihar.
A cewarsa, a matsayinmu na masu kishin jihar Kano, muna kira ga sabuwar gwamnati jiha da sauran masu ruwa da tsaki da su sa jihar Kano a gaba sama da nasu ra’ayoyin don a ciyar da jihar gaba.