Yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya tattauna ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandor.
Qin Gang ya bayyana cewa, Afirka ta Kudu, a matsayinta na shugabar kungiyar BRICS a wannan shekara, ta yi kokari, tare da gudanar da ayyuka masu dimbin fa’ida ga hadin gwiwar BRICS. Kasar Sin ta yaba da wannan matuka, kuma tana son ci gaba da ba da cikakken hadin kai ga aikin shugabancin kasar Afirka ta Kudu, da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa tare.
A nasa bangaren, Pandor ya bayyana cewa, kasar Afirka ta Kudu na son kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin bisa tsarin bangarori da dama kamar kasashen BRICS. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp