Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar har yanzu yana neman wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2023 da ke kara karatowa.
Tinubu, ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Abuja, a wurin bikin cikar kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shekara 60 a duniya.
- An Gano Gawar Tsohon Jakadan Nijeriya Da Ya Bace A Amurka
- Da Alamun Daliban Kano Ba Zasu Rubuta NECO A Bana Ba Kan Bashin 1.5 Da Ake Bin Gwamnatin Kano
Tsohon gwamnan na Jihar Legas, ya jinjinawa kakakin kan yadda ya taimaka wajen ci gaban dimokuradiyya a Nijeriya.
Idan za a iya tunawa, Tinubu ya dauki Kabiru Ibrahim Masari daga Jihar Katsina a matsayin abokin takara na wucin gadi.
Sai dai hakan ya haifar da ciwon baki, ga masu sharhi akan harkokin siyasa da kuma al’muran yau da kullum.
A baya-bayan nan Kabiru Masari, ya bayyana cewar zai iya ajiye takarar mataimakin dan takarar shugaban kasa na APC, matukar aka samu wanda ya fi shi nagarta.