Sake dawowar munanan hare- haren ta’addanci a Jihohin Sakkwato da Zamfara wadanda aka kai a makon jiya bayan daukar lokaci ba a shaidi dimbin asarar rayuka a lokaci daya ba, ya jefa al’umma cikin tashin hankali da zullumi musamman ganin cewar an fara samun zaman lafiya a jihohin.
A Jihar Sakkwato duk da cewar ko gabanin sabon harin ana fama da ayyukan ta’addancin a lokaci zuwa lokaci, maharan sun ci karen su ba babakka ne a ranar Asabar din makon jiya a inda suka kashe mutane 37 a Karamar Hukumar Tangaza, daya daga cikin Kananan Hukumomin da ke a Gabascin Sakkwato da sha’anin tsaro ya tabarbare a Jihar.
- EFCC Ta Kama ‘Yan Damfara 28 A Kuros Ribas
- Majalisar Dokokin Jihar Taraba Ta Bukaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tsaro Jihar
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar a ranar Lahadi ta tabbatar da mutuwar mutane 30 a garuruwan Raka, Bilingawa, Raka- Dutse, Jaba, Dabagi da Tsalewa duka a Karamar Hukumar Tangaza kamar yadda mukaddashin Kakakin Rundunar, Mataimakin Sufeto Ahmad Rufa’i ya bayyana.
Ya ce kafin kai harin wasu daga cikin manbobin kungiyar ‘yan sa- kai sun je har kauyen Azam a inda suka gargadi al’ummar Fulani da ke can. “To amma ‘yan sa- kan sun wuce gona da iri a inda suka rika dukan mutanen wadanda galibi Fulani ne, a kan wannan ne suka nemi taimako amma cikin rashin sa’a taimakon ya zo ne daga wasu da ke da makamai da ake zargin ‘yan ta’adda ne saman babura 20.”
“Ya kara da cewar bayan sun samu bayanin za a taho a taimaka masu sai suka koma garuruwansu. ‘Yan ta’addan kai tsaye suka kai wa ‘yan sa- kan hari a inda suka kashe mutane takwas a Raka, bakwai a Bilingawa, shida a Jaba, hudu a Dabagi, uku a Raka Dutse da biyu a Tsalewa.”
Kakakin ya kuma tabbatar da kai wani harin a ranar Asabar a wasu garuruwa da ke a Karamar Hukumar Gwadabawa duka a Gabascin Sakkwato.
A nasa bangaren, a tattaunawarsa da manema labarai, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tangaza, Honarabul Isa Salihu Kalanjeni ya bayyana cewar a yayin da suka yi kokarin bizne gawarwarkin a cikin dare sai ‘yan ta’addan suka dawo suka tarwatsa su, ya ce har zuwa safiya ba a iya yi wa wadanda aka kashe jana’iza ba.
“Laifin mutanen shi ne wai sun kasa biyan kudin harajin da aka dora masu. A kan wannan ne aka kawo masu hari aka kashe mutane 37 a yayin da wasu da dama suka samu raunuka tare da karbar magani a asibitin Gwadabawa.” In ji Kalanjeni.
Daukar matakin gaggawa kan sha’anin tsaro na kan gaba a cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya. Jim kadan da shigarsa ofis, Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin hukumomin tsaro da manufar yin duk mai yiyuwa domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya wanda a kan hakan jama’a na kyautata tsammanin za a samu canji kan yaki da ta’addanci nan da dan lokaci.
Faruwar lamarin wanda ya girgiza al’ummar Jihar Sakkwato ya sanya Gwamnan Jihar, Dakta Ahmed Aliyu katse ziyarar aiki da yake yi a Abuja a inda ya dawo ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro a Yammacin Litinin.
Gwamnan wanda Kakakinsa Abubakar Bawa ya bayyana cewar ya yi Allah- wadai da kai harin tare da alwashin daukar kwararan matakan tabbatar da tsaron rayukan al’umma da dukiyoyin su ya kuma yi alkawarin ci gaba da biyan kudin alawus da Gwamnatin Jiha ke biyan jami’an tsaro da ke aikin bayar da tsaro a wurare mafi hatsari.
Bawa ya bayyana cewar a taron an tattauna silar kai harin da hanyoyin kauce wa sake afkuwar hakan tare da tattauna yadda za a rika sa idanu ga ayyukan ‘yan sa- kai tare da tantance su domin fitar da baragurbi, an kuma aminta da cewar za su rika aiki kafada da kafada da jami’an tsaro.
Gwamnan wanda ya yi alkawarin magance matsalolin da jami’an tsaron ke fuskanta da suka hada da biyan bashin alawus na wata biyar, duba matsalar rashin ingantattun motoci da suke fama ya kuma bukaci al’ummar yankin da su taimaka wa jami’an tsaro da sahihan bayanan da za su rika taimaka masu wajen sauke nauyin da ke kan su.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar kwana daya da gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro, a ranar Talata Gwamna Aliyu ya jagoranci kakkarfar tawagar Gwamnati domin gani da ido tare da jajantawa wadanda lamarin ya shafa.
Gwamnan wanda ke tare da rakiyar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa da kaduwar yadda maharan suka yi wa al’ummarsa kisan gilla tare da alwashin daukar matakin da ya kamata domin ganin an magance afkuwar hakan a gaba.
Haka ma Gwamnan ya bayar da gudunmuwar abinci da kudi ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su a madadin Gwamnatin Jiha tare da rokon ubangiji ya gafarta masu.
Zamfara
Tabarbarewar sha’anin tsaro wanda bakidaya a Jihohin Arewa- Maso-Yamma ya fi kamari, a Jihar Zamfara; sababbin hare- hare na ci-gaba da faruwa ta hanyar kisan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
A ranar Asabar ‘yan ta’adda a Jihar sun kashe mutane 25 a Karamar Hukumar Maradun. Harin ya faru ne mako daya bayan da aka kashe wasu mutane 25 ciki har da jami’an sa- kai 16 a Gundumar Kanoma da ke a Karamar Hukumar Maru.
Mazauna yankin sun bayyana wa manema labarai cewar maharan sun kai farmaki a Jambako a inda suka kashe mutane 20. “Sun kawo hari a kauyen ne a saman babura da misalin karfe 2 na rana, suka fara bude wa jama’a wuta a inda jama’a suka tarwatse suna neman mafaka. Daga nan suka wuce kauyen Sakida a inda suka kashe mutane 5.” kamar yadda wani dan yankin Buhari Saminu ya bayyana.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana harin a matsayin mai muni tare da bayyana cewar Gwamnatinsa ba za ta zuba idanu tana kallon ‘yan ta’adda na kisan jama’a ba tare da magance matsalar ba.
Gwamnan wanda ya yi magana ta hannun Babban Mataimakinsa na Musamman kan Yada Labarai, Mustapha Jafaru Kaura ya bayyana cewar harin wanda bai kamata ba ya faru a daidai lokacin da gwamnatinsa ke matukar kokarin tsara yadda za ta shawo kan kalubalen matsalolin tsaro.
“An bayar da umurni ga shugabannin hukumomin tsaro da a cikin matakin gaggawa su kai jami’an tsaro a wuraren da lamarin ya shafa domin dakile sake faruwar asarar rayuka.” Ya bayyana.
A yayin da gwamnan ya yi ta’aziya ga iyalan da harin ya shafa, ya kuma jajanta wa wadanda suka samu raunuka a harin tare da rokon Allah ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu.
Bugu da kari Gwamna Lawal ya yi alkawarin tallafa wa iyalan wadanda aka kai wa harin kamar yadda ya bayyana a yayin da ya kai ziyarar jajantawa a yankin bayan kwanaki biyu.
Gwamnan wanda Mataimakinsa Malam Mani Malam Mumini ya wakilta ya bayyana cewar Gwamnatinsa tana iyakar kokari domin ganin ta shawo kan kalubalen tsaro a Jihar.
Ya ce Gwamnatin Jihar na kokarin duba hanyoyin masu kyau wajen tallafa wa mutane masu rauni da al’ummar da suka yi shekaru suna fama da hare- haren ta’addanci da satar shanu.
Mataimakin Gwamnan ya bayar da tallafin Gwamnatin Jihar na naira miliyan biyu ga wadanda lamarin ya shafa haka ma ya ce jami’ai za su fara aikin duba irin barna da asarar da aka yi wa jama’a tare da fitar da tsarin taimakawa.
Baya ga wannan, rahotanni sun nuna jami’an tsaron Rundunar Hadarin Daji sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda biyar da suka kai harin.
Wani babban jami’in soja ya bayyana wa gidan talabajin na Channels cewar jami’ansu da ke Bakura a yayin aikin sintiri sun samu sahihan bayanan kai hari a kauyen Rogoji da ke Bakura da Sakiddar Magaji a Jambako da ke Maradun.
“Da zuwan su kauyen, ‘yan ta’addan suka gudu, jami’anmu sun bi bayansu tare da yi masu barin wuta a inda aka kashe ‘yan ta’adda biyar. Sojojin sun samu nasarar karbe bindiga kirar AK- 47 guda biyu, alburusai da shanu, jakkai da awaki wadanda ba a tantance adadinsu ba.
Jihar Zamfara wadda a gwamnatocin baya gawurtattun ‘yan ta’adda suka mayar lahira kusa ta hanyar kisan gilla a duk lokacin da suka so tare da garkuwa da mutane da barnata dimbin dukiya; ga dukkanin alamu sabuwar gwamnatin jihar za ta sa kafar wando daya da mayakan a hobbasar kwazon samar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.