Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana cewa kokarin kakaba shugabanci a majalisa 10 da ake shirin kaddamarwa ba zai harfar wa da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da mai ido ba.
Kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed shi ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels tb a ranar Talata.
- Majalisar Dokokin Jihar Taraba Ta Bukaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tsaro Jihar
- Sin: Yin Katsa-landan Da Sanya Takunkumin Kashin Kai Ba Za Su Warware Batun Tsakiyar Afirka Ba
Hakeem ya ce, “Ba amfanin Shugaba Tinubu ba ne ya dora shugabannin a majalisar kasa. Ba ya cikin maslaha.
“Abin da ya fi dacewa shi ne, Tinubu ya nisanta kansa daga zaben shugabanin majalisar dattawa da mataimakinsa,” in ji shi.
Kakakin NEF ya jaddada cewa a bar ‘yan majalisar dattawa da ta wakilai su yanke hukunci wajen zaben shugabanninsu ba tare da tsoma bakin shugaban kasa ba.
Ya ce, “Ya kamata a bar ‘yan majalisa su yanke hukunci kan wurin da shugabanci zai nufa. Wannan ita ce ra’ayina da na tsaya a kai. Ban da ra’ayin cewa sai shugabancin majalisa ya koma yankin arewa. Na ce akwai sauran abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su.
“Idan ‘yan majalisa suka yanke hukunci cikin adalci, to shugabancin majalisa zai iya komawa kudu, mun tabbatar da haka. Sanna kuma zai iya zuwa arewa, babu wata matsala.”
Ya ce matsayin shugaban majalisar dattawa ana iya nada kowa kuma ana iya tsige shi.
Idan za a iya tuna jam’iyyar APC mai mulki ita ke da yawan kujeru a majalisar wakilai da suka kai 170 daga cikin kujeru 360 na zauren majalisar.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta zo ta biyu da kujeru sama da 100, jam’iyyar LP mai kujeru sama da 35, jam’iyyar NNPP ta samu kusan 20.
‘Yan majalisar APC da suka nuna sha’awarsu na zama shugaban majalisar wakilai dai sun hada da Benjamin Kalu, Ahmed Wase, Alhassan Ado-Doguwa, Yusuf Gagdi, Aliyu Betara, Tajudeen Abbas, Abdulraheem Olawuyi, Sani Jaji, Gimbiya Onuoha da dai sauransu.
Haka kuma a bangaren majalisar dattawa kuwa, masu sha’awar zama shugaban majalisar dattawa sun hada da Sanata Abdulaziz Yari, Orji Kalu, Godswill Akpabio da dai sauransu.
Sai dai kuma jam’iyyar APC ta tsayar da Akpabio daga yankin kudu maso kudu a matsayin shugaban majalisar dattawa da kuma Barau Jibrin daga yankin arewa maso yamma a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Jam’iyyar ta kuma tsayar da shugabancin majalisar wakilai zuwa arewa maso yamma wanda ta bai wa Abass, da mataimakin shugaban majalisar daga kudu maso gabas da ta bai wa Kalu.
Sai dai kuma hukuncin jam’iyyar ta gamu da rashin amincewa daga mafi yawancin ‘ya’yan jam’iyyar APC, inda suka bukaci a sake duba tsarin da zai shafi shiyyar arewa ta tsakiya ba wai matsayi biyu na yankin krewa maso yamma ba.
Hujjarsu ita ce arewa maso yamma sun bai wa shugaban kasa kuri’a mafi girma don haka ya cancanci a biya su diyya na kai shugabancin majalisar ga yankin.