• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NIS Ta Bi Ƙa’ida Sau Da Ƙafa Wajen Bai Wa David Nwamina Fasfo – CGI Isah Jere

by yahuzajere
3 years ago
David Nwamina

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), ta tabbatar da cewa ta bi ƙa’ida sau da ƙafa wajen bayar da Fasfon Nijeriya ga ɗan samarin nan, Mista David Ukpo Nwamina da ake ƙiƙi-ƙaƙa a kansa game da batun cire wata gava a jikinsa domin dasa wa wata yarinya mara lafiya, ‘yar gidan tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu.

Wata sanarwar manema labarai da Shugaban NIS, CGI Isah Idris Jere ya fitar tare da rattaba hannu da kansa, ta yi bayanin cewa yamaɗiɗin da wasu ke yaɗawa, “cewa hukumar ba ta tantance takardun wanda aka bai wa fasfon yadda ya kamata ba, ba gaskiya ba ne illa ƙazafi da wasu suka kitsa don kawai su shafa wa hukumar kashin kaji a vata mata suna.

  • Yajin Aikin ASUU: Dalibai Sun Yi Barazanar Rufe Tituna, Tashoshin Jirgin Sama Da Na Kasa
  • Da Aka Gama Rarraba Wa Deliget Kudi, Sai Kuma Me? (Ra’ayinmu)

“Don haka gaskiyar abin da ya faru game da lamarin shi ne, shi wanda ake magana a kansa, Mista David Ukpo Nwamina ya gabatar da buƙatarsa ta sabon fasfo da aka inganta kuma ya biya kuɗin fasfon ta manhajar intanet wanda bayan haka ne ya tafi Ofishin Fasfo na Abuja da ke Gwagwalada a ranar 2 ga Nuwambar 2021 domin amsa tambayoyi. Domin ƙarfafa samun fasfon nasa, Mista David Nwamina ya gabatar da dukkan takardun ƙa’ida da suka wajaba, da suka haɗa da takardar haihuwarsa wadda Hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta ba shi, da ta nuna an haife shi a ranar 12 ga Oktobar 2000, sannan bayanan shaidar haihuwarsa ta lambar ɗan ƙasa wadda Hukumar NIMC ta ba shi, sun yi daidai da na takardar haihuwarsa sai kuma takardar shaidar asalinsa wadda Ofishin Gwamnatin Jihar Ebonyi na Abuja ya ba shi da kuma takardar shaidar mutumin da ya tsaya masa da aka rattaba wa hannu kamar yadda ya kamata.”

Saboda haka bisa waɗannan hujjoji, NIS tace tana sanar da jama’a cewa ba ta wallafa ranar haihuwa ko wasu bayanai a duk wani fasfon Nijeriya har sai an tantance su yadda ya kamata tare da tantance shi kansa mai neman fasfo. “Don haka batun Mista Nwamina ba zai zama daban ko na ɗanmowa ba.”

Har ila yau, Hukumar ta NIS ta tabbatar wa da al’umma irin duƙufar da ta yi wajen kare mutuncin fasfon Nijeriya, kana ta yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jama’a su guji furta irin waɗannan ƙarairayi domin za su iya zubar da kimar hukumar a idon duniya.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

  • https://portal.immigration.gov.ng/

Mista David Ukpo Nwamina dai na can Ingila ana ci gaba da bincike a kansa da wanda abin ya shafa Sanata Ike Ekweremadu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu
Labarai

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
Labarai

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
Labarai

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Next Post
Na Dakatar Da Ayyukan Banga Har Gwamnati Ta Binciki Dalilin Kamani – Manta

Na Dakatar Da Ayyukan Banga Har Gwamnati Ta Binciki Dalilin Kamani - Manta

LABARAI MASU NASABA

Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma

October 24, 2025
An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

October 24, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

October 24, 2025
Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.