Babban Sufeto na ‘yansandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya umarci kwamishinan ‘yansandan jihar Filato, Bartholomew Onyeka da ya rufe dukkanin sakataroriyar kananan hukumomi 17 da ke jihar.
Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya amince da dakatar da shugabannin kananan hukumomi 17 na kananan hukumomi 17 da wa’adinsu bai cika ba, lamarin sam bai yiwa jam’iyyar adawa ta APC dadi ba a Jihar.
Sabida, akasarin shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar, zababbu ne a karkashin jam’iyyar APC, don haka suka bijirewa umurnin gwamnan, suka ki ficewa daga ofisoshinsu su barwa kwamitocin rikon kwarya da ke wakiltar PDP. Wannan takaddama na barazana ga tsaron jihar.
Rundunar ‘yansandan jihar a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar (PPRO), DSP Alfred Alabo ya fitar a Jos, ta ce, wannan matakin da rundunar ‘yansandan ta dauka ya zama dole sakamakon rudani da takaddama da ke tsakanin shugabannin kananan hukumomin.
Sanarwar ta kara da cewa, Akwai kuma yiwuwar barazanar cewa, magoya bayan shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar, na iya tayar da hankulan jama’a wanda zai kai ga asarar rayuka da dukiyoyi a jihar.