Masu sharhin al’amurar siyasa suna ganin akwai jan aiki a gaban shugabannin majalisar dokakin Nijeriya ta 10 wadanda suka hada da samun goyon bayan dukkan ‘yan majalsa.
Sanin kowane akwai rarrabuwar kai a majalisun dokokin Nijeriya, musamman a daidai lokacin da aka fafata zabe wasu suka yi nasara, yayin da wasu suka yi rashin nasara.
- Yariman Bakura Ya Taya Akpabio Murnar Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10
- Sin: Bai Kamata A Shigar Da Salon Fito-na-fito Cikin Tsarin Ayyukan Hukumomin Hada-hadar Kudi Na Kasa Da Kasa Ba
Masu sharhin suna ganin zai yi wahala ‘yan majalisar da suka fadi su amince da sabbin shugabannin, saboda tun lokacin da jam’iyyar APC da Shugaban kasa Tinubu suna fito karara suka bayyana ‘yan takarar da suke bukatan zama shugabanin majalisar dokokin Nijeriya aka samu baraka da sauran ‘ya’yan jam’iyya da ma ‘yan dawa, inda suke ganin ana kokarin katsalandan a sha’anin shugabancin majalisa.
Masana suna ganin cewa idan har dan takarar da shugaban kasa yake so suka samu nasara, to majalisar za ta kasance ‘yan amshin shata, wato duk kudurin shugaban kasa za a aiwatar masa da shi ba tare da samun turjiya ba.
Amma kuma wasu na ganin duk da cewa ‘yan takarar shugaban kasa ne suka yi nasara, shugaban kasa yana iya samun turjiya a kan kudurinsa, domin kuwa sai an samu amincewa daga sauran ‘yan majalisa kafin a amince da kudurin da shugaban kasa ya bijiro da shi.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan sabbin shugabannin majalisar sun gana da shugaban kasa, Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajuddeen ya jaddada cewa ba za su zama ‘yan koron bangaren zartaswa ba, “ba ‘yan amshin shata za mu zama ba, duk abin da bangaren zartaswa ya aiko za mu yi masa duba na tsakanaki domin tabbatar da cewa ya dace da kudirin kawo wa al’umma ci gaba.”
Sai dai kuma, a duk lokacin da aka samu sabbin shugabanni na majalisa, sukan fadi haka amma daga baya aikinsu ya saba da abin da suka fada. Shi ya sa yanzu ‘Yan Nijeriya za su zuba na mujiya su gani, ‘yan amshin shata aka zaba ko masu kishin kasa? Lokaci ne kadai zai tabbatar da haka.