Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka saba shiryawa a yau cewa, kasar Sin tana farin cikin ganin kamfanonin kasashen waje suna zuba jari da yin kasuwanci a kasar, da samun damar ci gaba tare.
Tun daga farkon wannan shekara, manyan jami’an shahararrun kamfanonin kasashen waje da dama sun ziyarci kasar Sin, wadanda suka shafi motoci, sarrafa kayayyaki, likitanci, hada-hadar kudi, fasahar kayan laturoni da sauran fannoni.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, a baya-bayan nan ne wasu kungiyoyin kasuwanci na kasashen waje dake kasar Sin suka fitar da rahotannin dake nuna cewa, har yanzu yawancin kamfanonin kasashen waje da aka yi nazari a kansu na da yakini kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da yin aiki tare da sauran kasashen duniya, don cimma nasarori tare. (Yahaya)