Akalla manoma 50 ne aka ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun hallaka su a yankuna da ban da ban da ke a cikin karamar hukumar Rafi da ke a jihar Nija, inda harin ya janyo daruruan wasu mazauna yankimn suka arce daga gidajen su.
An ruwaito cewa, maharani sun kai harin ne a makon da ya gabata.
- Zan Yi Aiki A Bayyane Tare Da Shugabannin Majalisa Ta 10 – Tinubu
- Jakadun Kasashen Afirka Sun Bayyana Gamsuwa Ga Makomar Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daya daga cikin manoman mai suna Abdullahi Usman, ya bayyana cewa, maharan su sama da 100 akan Babura kimanin, 50, sun kai harin a kauyukan ne da misalign karfi 2 na ranar Jum’ar da ta gabata, inda suka kai har zuwa safiyar Asabar suna cin Karensu babu babbaka.
Abdullahi ya bayyana cewa, maharani sun dawo da kai farmakin su da ne da karfi, inda ya sanar da cewa, harin na sa kara lalata al’amura a kaukan.
“Maharan su sama da 100 akan Babura kimanin , 50, sun kai harin a kauyukan ne da misalign karfi 2 na ranar Jum’ar da ta gabata, inda suka kai har zuwa safiyar Asabar suna cin Karensu babu babbaka.”
“Sun kai harin a kauyukan ne da misalign karfi 2 na ranar Jum’ar da ta gabata, inda suka kai har zuwa safiyar Asabar suna cin Karensu babu babbaka.”
Shi ma wani manomin wanda ya arace daga kauyen mai suna Abdulmalik Usman, ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-hare a kauyaka da dama da ke a cikin jihar, ciki har da a Gidigori, Gando, Kusherki.
A cewarsa, ‘yan bidigar sun kuma yi awon gaba da Akuyoyin mu, Raguna da Shanu, inda ya ci gaba da cewa, bayan sun kai harin a kauyen mu, sun kuma kusta kuyukan Madaka, Hanna-Wanka, Kukoki.
“’Yan bindigar sun kai hare-hare a kauyaka da dama da ke a cikin jihar, ciki har da a Gidigori, Gando, Kusherki.”
A cewarsa, daukacin karamar huikumar Rafi a yanzu babu wata kariya, sama da manoma 50 ne aka kashe a Rafi a makon da ya wuce.
Masu manazuna kuyukan sun yi zargin cewa, darun soji da ke a Kagara da Pandogari, ba su kawa wa kauyakan dauki ba a lokacin da maharani suka kai masu harin, inda ya kara da cewa, sojijin suna yin sintin su ne kawai a garin Kagara.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Wasiu Abiodun ya bayyana cewa, rundunar ta tura jami’anta zuwa kauykan da aka kai hare-haren don kwantra da kura.