Shugabanni da manyan jami’ai na kasashen Afirka ta Kudu, da Masar, da Senegal, da Congo Brazaville, da Comoros, da Zambia, da Uganda a madadin sauran kasashen Afirka, sun ziyarci kasashen Ukraine da Rasha a kwanakin baya, inda suka gana da shugabannin kasashen, tare da gabatar da shawarar maido da zaman lafiya. Wannan ziyara na tare da ma’ana ta musamman.
Kamar yadda Murithi Mutiga, darekta mai kula da harkokin nahiyar Afirka na kungiyar daidaita rikicin kasa da kasa (ICG), ya fada, wannan wani aikin shiga tsakani ne da wasu kasashen dake nahiyar Afirka suka yi a hadin gwiwar gudanarwa a wajen nahiyar Afirka, wanda ba safai a kan gan shi ba. Saboda haka batun ya nuna yadda kasashen Afirka ke samar da karin tasiri a harkokin kasa da kasa.
Sai dai a nasu bangare, kafofin watsa labaru na kasashen yamma ba su dauki wannan ziyara da muhimmanci ba, har ma sun nuna shakku kan ma’anarta. Inda kamfanin BBC na kasar Birtaniya ya yi sharhin cewa, “kamar ba a kai ziyarar a lokacin da ya dace ba, ganin yadda bangaren Kyiv take kokarin kaddamar da hare-hare” “Ko ana neman cimma wani buri da wannan ziyara ne?” Kana kamfanin AP na kasar Amurka ya ce, “Wadannan shugabannin kasashen Afirka sun kira kansu ‘tawagar neman zaman lafiya’, amma ba a ga wani sakamakon da aka cimma ba har bayan da ganawarsu da shugabannin Ukraine da Rasha ta kai karshe.”
Hakika zancen kasashen yamma bai ba ni mamaki ba. Saboda na san sun riga sun fada cikin yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha. A ganinsu, dole ne a nuna goyon baya ga Ukraine, da yin Allah wadai da kasar Rasha. Sai dai maimakon haka, kasashen Afirka sun zabi matsayi na ba ruwanmu, da kokarin neman ganin dawowar zaman lafiya.
Amma a nata bangare, kasar Sin na da matsayin iri daya da na kasashen Afirka. A ranar 24 ga watan Fabrairun bana, ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta gabatar da wata takarda don bayyana matsayin kasar Sin game da yadda za a daidaita rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. Kana tun daga watan Mayun bana, kasar Sin ta tura wani manzon musamman don ya ziyarci Ukraine, da Poland, da Faransa, da Jamus, da hedkwatar kungiyar kasashen Turai ta EU, gami da kasar Rasha, inda ya yi kokarin lallashin bangarori daban daban don a maido da zaman lafiya.
A ganin kasar Sin, ya kamata a lura da damuwar kowane bangare kan tsaro, da nuna goyon baya ga duk wani matakin da zai taimakawa daidaita rikici ta hanyar sulhu.
Yanzu ko da yake akwai wuya a sanya bangarori masu ruwa da tsaki su zauna a gaban teburin shawarwari, amma abun da ya fi muhimmanci shi ne a yi kokarin samar da sharadin kawo karshen rikici sannu a hankali. Idan muka yi tsokaci bisa ra’ayin kasar Sin, to, kokarin sulhuntawa da kasashen Afirka suka yi babbar gudunmowa ce dake samar da damar daidaita rikici cikin ruwan sanyi a nan gaba.
Sa’an nan, a ganina, ziyarar shugabanni da jami’ai na Afirka a wannan karo ta nuna tasirin kasashen Afirka a duniya, gami da yadda kasashen Afirka suke dogaro da kansu a fannin tsara manufofin diplomasiyya.
’Yan Afirka ba za su maimaita abun da ya faru a lokacin manyan yake-yaken duniya guda 2 ba, inda suka halarci yaki da sadaukar da rayukansu, bisa umarnin da Turawa ‘yan mulkin mallaka suka yi. Yanzu sun iya gabatar da wata manufar da ta sha bamban da ta kasashen yamma, bisa la’akari da moriyar kansu.
Ban da haka, ko kun taba tunanin mene ne dalilin da ya sa kasashe masu tasowa irinsu kasashen Afirka, da Sin, da Indonesia, da Brazil, suka fi son ganin tsagaitar bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine? A ganina, wannan shi ne domin akwai bambanci tsakanin kasashe masu tasowa da kasashen yamma, ta fuskar bukatunsu.
Kasashen yamma sun yi takama cewa sun fi sauran kasashe samun dimokuradiyya da ’yanci, amma a hakika suna karkashin sarrafawar wata babbar kasar dake kokarin yin babakere a duniya. Bukatarsu ita ce samun cikakken ikon tabbatar da yadda ake raba moriya a duniya, don kare tsarin duniya da ya mai da kasashen yamma a matsayin cibiya. Wannan yunkuri ya sa kasashen yamma kokarin neman “abokan gaba” a duniya da kai musu hari, ba tare da tsayawa ba.
Yayin da a nasu bangare, kasashe masu tasowa sun fi bukatar tsarin duniya mai adalci, wanda ya kunshi mabambantan bangarori masu fada a ji, da wani muhalli mai zaman lafiya da karko, inda ake iya samun ci gaban kasa mai dorewa. Idan mun yi tsokaci bisa wannan ra’ayi, za mu san cewa, kasashe masu tasowa sun fi kaunar zaman lafiya. Sai dai wani lokaci ma, sauran kasashe su kan yi musu shisshigi, da tilasta musu shiga cikin yaki.
Wani abun da ya kamata su kasashen yamma su yi la’akari a kansa, shi ne, dabarar da suka dauka, ta tayar da yaki a sauran kasashe don tabbatar da tsaron kai, da lahanta moriyar sauran kasashe don kare matsayin kansu a duniya, wato raunana saura don kare moriyar kai, wannan dabara ko za ta iya dorewa? (Bello Wang)