ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Zaman Lafiya Ta Hanyar Tattaunawa” Ita Ce Kawai Mafita Ga Gabas Ta Tsakiya

by CMG Hausa
3 years ago
Gabas ta Tsakiya

A ranar 14 ga watan Yuni, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas a nan birnin Beijing. Sun sanar da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Falasdinu.

Shugaba Xi ya gabatar da shawarwari mai kunshe da abubuwa uku na warware batun Falasdinu. Ya bayyana cewa babbar hanyar warware batun Falasdinawa ita ce kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta wacce ke da cikakken ikon mallakar kai a bisa yarjejeniyar kan iyakoki ta shekarar 1967 da kuma gabashin Kudus a matsayin babban birninta.

  • Shugaba Xi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Ya kamata a biya bukatun tattalin arziki da rayuwar Falasdinawa, sannan kasashen duniya su kara kaimi wajen taimakon raya kasa da taimakon jin kai ga Falasdinu. Kuma a karshe, yana da muhimmanci a kiyaye hanyar da ta dace na tattaunawar da za ta kai ga zaman lafiya.

ADVERTISEMENT

Hanyar da kasar Sin ke bi na samun zaman lafiya ta samo asali ne daga tsohuwar hikimar kasar Sin, kamar yadda yake bayyane a cikin wadannan kalamai: “Bai kamata masu karfi da masu kudi su rika zaluntar marasa karfi da matalauta ba”, kuma “duk kasar da ke takama da karfin yaki, duk girmanta, daga karshe za ta durkushe.” Wadannan kalmomi masu zurfi suna misalta kimar kasar Sin yayin da take tafiyar da tsarin kasa da kasa mai sarkakiya da rashin kwanciyar hankali, tare da neman hanyar zaman lafiya da ci gaba, ta hanyar tattaunawa da mutunta ’yancin juna ba tare da katsalandan ko shisshigi ba.

Abin da ke tattare da irin wannan yunkurin na kasar Sin shi ne wasu suka mayar da batun tattaunawa game da babbar hamayya tsakanin manyan tattalin arzikin duniya guda biyu. A wannan yanayi, an mayar da hankali kan Sin da Amurka a Gabas ta Tsakiya, da tabarbarewar alakar da ke tsakaninsu. Sanin kowa ne cewa Amurka da Isra’ila sun kulla alaka mai karfi ta tsaro, da tattalin arziki da siyasa.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Kuma idan aka yi la’akari da yanayin siyasa mai sarkakiya a yankin, yin nazari game da dangantakar abota tsakanin kasar Sin da Falasdinu, wani zai dauka kasar Sin na kalubalantar Amurka ne.

Kasar Sin ba ta da sha’awar kalubalantar Amurka a Gabas ta Tsakiya ko kuma a ko’ina. Tasirin da Amurka ke da shi a yankin na kara raguwa saboda tsarin siyasarta da bukatunta. Babu wanda za a zarga da sanyaya dangantakar Amurka da yankin Gabas ta Tsakiya face zabin da Amurka ta yiwa kanta.

Akidar Confucius ta kayyade cewa “ya kamata mutum ya nemi jituwa a cikin bambance-bambance kuma kada ya yi wa wasu abin da ba zai so a masa ba.” Burin kasar Sin shi ne ta samar da daidaito a wannan duniyar da ke cike da bambance-bambance. Kuma tana taimaka wa kasashen Gabas ta Tsakiya da hakan. (Yahaya Babs)

Gabas ta Tsakiya
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Johann Rupert Ya Doke Dangote A Matsayin Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi A Afirka

Johann Rupert Ya Doke Dangote A Matsayin Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi A Afirka

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.