Yayin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya kammala ziyarar yini biyu a kasar Sin, masharhanta na ci gaba da tsokaci game da tasirin da wannan ziyara ka iya haifarwa a fannin kyautatuwar alakar kasashen Sin da Amurka.
Yayin ziyarar da mista Blinken ya gudanar a kasar Sin a ranaikun 18 da 19 ga watan nan na Yuni, jagororin kasashen biyu sun amince da aiwatar da muhimman kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron birnin Bali na kasar Indonesia a watan Nuwambar bara. Idan ba a manta ba a wancan lokaci shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun amince su aiwatar da dukkanin matakan da suka kamata, na shawo kan sabani, da bunkasa tattaunawa, da musaya da hadin gwiwa tsakanin kasashen su.
Kaza lika a yayin ziyarar ta mista Blinken a Beijing, ya zanta da babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Qin Gang, inda suka sake jaddada matsayin kasashensu na daukar dukkanin matakan da suka wajaba na gyara alakar kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.
Ko shakka babu alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, da tasirin gaske a fannin raya ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummun duniya baki daya. To sai dai kuma wadannan kasashe za su iya kaiwa ga cimma kyakkyawar alakar da suke fata ne kadai, idan suka amince su mutunta juna, tare da warware sabani, da amincewa da banbance-banbancen dake tsakaninsu ta fuskar siyasa, da al’adu, da tafarkin neman ci gaba.
Muna iya cewa, ziyarar ta mista Blinken a wannan karo tana da ma’anar gaske a tarihin dangantakar Sin da Amurka, duba da yadda ta baiwa kasashen biyu damar zurfafa tattaunawa, da shawarwari masu ma’ana, wadanda ka iya ingiza kyautatuwar alaka, da warware wasu muhimman batutuwa dake jan hankalinsu, musamman wadanda suka jibanci harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi.
Wani abun lura ma a nan shi ne wannan ziyara ta Blinken, ita ce ta farko da wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka ya gudanar a kasar Sin, tun bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya hau karagar shugabancin Amurka a 2021. Ana kuma kallonta a matsayin dama ta tattauna matakan kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu, wadda a bayan-bayan nan take kara sukurkucewa.
Har ila yau ziyarar ta gudana watanni biyar bayan da aka dage ziyarar da mista Blinken din ya shirya gudanarwa a Sin, sakamakon zargin da Amurka ta yi cewa Sin ce ke mallakar wani bala-balan na leken asiri, wanda ya yi shawagi a sararin samaniyar Amurka, duk da musanta hakan da bangaren Sin ya yi.
Masu fashin baki na ganin idan har makasudin wannan ziyara ta mista Blinken ita ce bude kofar kyautata hanyoyin inganta hulda tsakanin manyan ƙasashen biyu, bayan sabanin da aka samu kan waccan balan-balan, da ma batun wanzar da zaman lafiya a zirin Taiwan, ko kamata ya yi a yanzu sassan biyu su cika alkawuran da suka yi yayin wannan ziyara mai muhimmanci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, yayin wannan ziyara, Beijing da Washington sun amince su ci gaba da gudanar da musaya tsakanin manyan jami’an su, domin cimma burin da suka sanya gaba. Har ma mista Blinken ya gayyaci Qin Gang, da ya ziyarci Amurka, kuma tuni Qin din ya bayyana amincewa da hakan.
Baya ga batun ci gaba da musayar ra’ayoyi tsakanin kusoshin gwamnatocin kasashen biyu, an kuma amince da fadada musayar al’adu da ilimi, tare da ci gaba da tattauna batun kara adadin jiragen sama dake zirga-zirga tsakanin kasashen biyu. Kari kan hakan akwai batun bude kofofin musayar dalibai, da masana, da ’yan kasuwa, tare da samar da kyakkyawan yanayin aiwatar da hakan.
Kafin ambata wadannan matakai dai, Qin ya koka game da yadda dangantakar Sin da Amurka ta yi matukar tsami a shekarun baya bayan nan, zuwa wani yanayi mafi muni tun bayan kulla ta, wanda hakan ya sabawa manyan ginshikan cimma moriyar kasashen da al’ummun su, kaza lika hakan ya saba da fatan sassan kasa da kasa don gane da yanayin da ya dace kasashen biyu su kasance a kai.
A bangaren kasar Sin, manufofin ta don gan da alaka da Amurka, a iya cewa ba su sauya ba, domin kuwa ministan harkokin wajen Sin din ya sake jaddada su, inda ya bayyana kiran da kasar Sin ta sha yi ga Amurka, na ta rungumi matakan tattaunawa da wanzar da daidaito, ta amince da salon raya dangantaka tsakaninta da Sin bisa martaba juna, da tafiya tare a yanayi na zaman lafiya da lumana, da martaba ikon cimma gajiyar kasashen ba tare da fito na fito, ko shiga sabon salon cacar baka ba, kamar dai yadda shugaban na Sin ya gabatar da wannan shawara yayin taron Bali na watan Nuwambar bara.
Har ila yau, idan an samu wani rashin fahimtar juna ko sabani, Sin na fatan Amurka za ta amince da hawan teburin shawara, ta yadda za a kai ga warware komai bisa salo na siyasa da hangen nesa.
Wani batu mai jan hankali ma shi ne batun Taiwan, wanda a wannan karo ma bangaren kasar Sin ya sake ayyana shi a matsayin jigon kyautata alakar kasashen biyu. A wannan bangaren Sin ta fayyace cewa, batun Taiwan harka ce ta cikin gidan kasar Sin wadda bai kamata wani bangare na waje ya tsoma baki cikin ta ba. Kuma idan an kalli batun ta wata mahangar, yana da alaka da babbar manufar siyasar kasar Sin ta kasacewar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya”. Don haka duk wani yunkuri na neman ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, zai iya haifar da barazana ga huldar Sin da bangaren dake marawa hakan baya. Don haka a wannan karo ma ministan harkokin wajen na Sin ya sake nanata kira ga gwamnatin Amurka, da ta rungumi wannan manufa ta kasancewar Sin daya tak a duniya, da ma abubuwan dake kunshe cikin yarjeniyoyin nan uku na hadin gwiwa da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, masu karfafa adawa da duk wani yunkuri na tallafawa “samun ’yancin kan yankin Taiwan “.
Baya ga ganawa da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang a ranar Lahadi, mista Blinken ya kuma zanta da shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Litinin da yamma, gabanin kammala wannan ziyara mai cike da tarihi. A lokacin ne kuma shugaba Xi Jinping ya bayyanawa babban jami’in diflomasiyyar Amurkan cewa, duniya na da fadin da ya isa dukkanin bangarorinta su ci gajiya, ba tare da shiga cacar baka, ko wata takara maras tsafta ba. Kuma akwai bukatar hada kai da juna tsakanin kasashen duniya, domin cimma nasarar bunkasa rayuwar daukacin bil Adama.
Shugaban na Sin ya kuma ce a matsayin su na manyan kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki, kasashen Sin da Amurka na iya cimma muradunsu na bunkasuwa ba tare da mayar da juna baya ba. Bugu da kari, sassan biyu za su iya cimma wannan nasara ne kadai, idan sun rungumi salon mutunta juna, da wanzar da zaman lafiya da lumana tsakaninsu, wanda hakan ya yi daidai da muradin sassan kasa da kasa, na ganin ci gaban alakar sassan biyu ta dore lami lafiya.
Idan kuwa muka waiwayi bangaren Amurka, za mu ga cewa a wannan karo ma, sakataren wajen nata ya kafe cewa, kasarsa ba ta sauya matsaya ba kan manufofin ta da suka shafi kasar Sin, wato dai har yanzu Amurka tana kan bakanta na yin hadin gwiwa da bangaren Sin, ta yadda za su kai ga kyautata fahimtar juna, da warware matsaloli, da rashin jituwa da suke fuskanta, da yaukaka musaya, da hadin gwiwa, daidai da shawarwarin da shugabanninsu suka cimma a taron tsibirin Bali da ya gudana a bara.
Wani abun lura a nan shi ne, a wannan karo ziyarar mista Blinken a kasar Sin za ta zamo tamkar manuniya game da gaskiyar burin kasar sa na cimma muradun da aka sa gaba, kasancewar sa tsohon jami’in diflomasiyyar Amurka da ya ga jiya yake kuma ganin yau.
Idan ba mu manta ba, mista Bliken ya ziyarci kasar Sin a karon farko ne a shekarar 1996, lokacin da yake rike da mukamin mamba a matsalisar tsaron Amurka, karkashin gwamnatin shugaba Bill Clinton. Ya kuma kara zuwa kasar Sin a mulkin tsohuwar gwamnatin Barack Obama a shekarar 2015, lokacin yana mataimakin sakataren wajen waccan gwamnati da ta shude. Kuma tun bayan kasancewarsa sakataren wajen Amurka a watan Janairun shekarar 2021, karkashin gwamnatin Joe Biden mai ci, ya sha yayata amincewarsa ga manufar kyautata dangantakar kasarsa da Sin, bisa ginshikai uku; wato zuba jari, da daidaita tafiya, da kuma yin takara mai ma’ana. Yana mai bayyana Sin a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki, wadda ta jima da zama babban abokiyar takarar Amurka, duk da Beijing ba ta amince da matsayar Amurka game da batun takara ba.
Lura da wannan tarihi, na kasancewar mista Blinken kwararre, kuma dadadden jami’in diflomasiyyar Amurka, ana iya cewa Amurka na da duk kwarewa da fahimtar inda aka dosa, don gane da sabanin da ake gani yanzu haka tsakaninta da Sin, kuma duniya na zuba ido don ganin ko a wannan karo al’amura za su sauya ko a’a.
Masharhanta na ganin lokaci ne kawai zai nuna ko Amurka za ta sauka daga matsayinta na yin baki biyu, tare da aiwatar da matakan da suka dace ko a’a.
Kaza lika, akwai masu ganin ziyarar mista Blinken ta wannan karo ta samar da zarafi ga kasashen biyu, na ci gaba da tuntubar juna, maimakon fito na fito da cacar baka ta kafofin watsa labarai, kuma hakan na iya dorewa, idan bangarorin biyu suka ci gaba da tattaunawa da gudanar da shawarwari yadda ya kamata. Bugu da kari a wannan karo, ana fatan Amurka za ta yi la’akari da sakamakon ziyarar wajen taka birki ga tabarbarewar dangantakarta da Sin, ko da kuwa a wasu fannoni ne kalilan. Da yake Bahaushe kan ce “Da babu gwara ba dadi”.
Amma fa masu dari-dari game da sakamakon da za a iya gani a kasa na cewa, manufofin Amurka na baya bayan nan, da suka hada da kallon kasar Sin a matsayin abokiyar takara da jayayya, da daukar ta a matsayin wadda ya zama wajibi a kaucewa hadarin ta, ko wadda dole a warware tasirin ta, dukkanin su na nuni ga irin yadda Amurkan ta ki tsayawa bangare guda, kan wannan batu na dakile yanayin kara tabarbarewar dangantakarta da kasar Sin.
Cikin wadanda suka tofa albarkacin bakin su kan hakan, akwai mista Michael Swaine, babban masani game da harkokin da suka shafi gabashin Asiya, a cibiyar “Quincy” mai rajin bunkasa wanzar da fahimtar juna, wanda ya jinjinawa ziyarar mista Blinken din ta wannan karo, kuma a ganinsa Washington ta nuna aniyar farfado da daidaito a alakarta da Sin. Yana kuma ganin muddin Washington da Beijing da gaske suke suna son ganin bayan rashin fahimtar juna, to ya zama dole su karfafa manufofin su na diflomasiyya, tun kafin sabani ya rikide zuwa fito na fito da ba a fata. (Saminu Alhassan)