Shugaban ma’aikatan jihar Kano, Alhaji Usman Bala, da Akanta-janar na jihar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam tare da kwamishinan yada labarai, Alhaji Baba Halilu Dantiye, sun yunkuro domin fayyace dakatar da albashin ma’aikatan jihar 10,000.
LEADERSHIP ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da albashin ma’aikatan gwamnati jihar dubu 10 wadanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta dauka kafin barin gwamnati.
- Sarkin Noman Gaya Ya Nemi Gwamna Abba Ya Bullo Da Sabon Tsarin Bunkasa Noma
- Ban Yi Nadamar Rusau A Kano Ba -Gwamnan Kano
Da suke magana a yayin tattaunawa da ‘yan jarida, shugaban ma’aikatan ya ce matakin da aka dauka na dakatar da biyan albashin an yi bisa dacewa da tsari da ka’idar ma’aikata.
A cewarsa an kafa babban kwamitin da zai yi bincike kan sahihancin takardu da hanyoyin da aka bi wajen daukan ma’aikatan aiki.
Bala, ya ce babu wata matsala, nan da wani lokaci za su dawo da biyan ma’aikatan da aka tantance sannan aka tabbatar da ingancinsu.
“Wadanda kuma ba su cancanta ba ko kuma wadanda suka samu aikin ta wasu hanyoyi na son zuciya za a nuna musu hanyar da za su fice saboda gwamnatin ba za ta bari a lalata tsarin aiki ba”.
Shi kuwa Akanta-Janar ya nuna damuwarsa kan halin da ake ciki a bangaren ma’aikatan gwamnati.
“Gwamnatin NNPP karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta zo ne da sabbin tsare-tsare da kyawawan manufofin yadda za a gudanar da gwamnati bisa gaskiya don kaucewa rashawa a tsakanin al’ummar jihar.”