ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Amurka Ta Sake Komawa UNESCO Bayan Da Ta Sha Ficewa Daga Hukumar?

by CMG Hausa
2 years ago
UNESCO

Amurka za ta sake komawa hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adu ta MDD, wato UNESCO a takaice. 

A ranar 30 ga watan Yuni, an zartas da wani daftarin kuduri yayin taron musamman na babban taron UNESCO, inda aka amince da maido da kujerar kasar Amurka a hukumar tun daga watan Yulin da ake ciki daga dukkanin fannoni. Hakan nan ya zama karo na uku da Amurka za ta kasance mamban hukumar, wato bayan da ta fice daga hukumar a shekarar 1984 da ta 2018.

  • Sin: Ya Dace Amurka Ta Ingiza Hada Kan UNESCO Bayan Dawowarta Hukumar

Amma me ya sa Amurka ta sake komawa hukumar? Me ya sa kuma ta sha komawa bayan ficewa?

ADVERTISEMENT

Wata kila muna iya gano amsar tambayar daga jawabin da mataimakin sakataren harkokin wajen kasar John Bass ya yi, a gun taron manema labarai da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta gudanar a watan Maris da ya gabata, inda ya ce, a ganin gwamnatin kasar Amurka, komawa hukumar UNESCO zai taimakawa Amurka wajen takarar da take yi da kasar Sin a duniya.

A hakika, a cikin ’yan shekarun baya, Amurka ta sha ficewa da kuma komawa hukumomi, da yarjejeniyoyi na kasa da kasa. Idan ba a manta ba, baya ga UNESCO, Amurka ta kuma fice daga yarjejeniyar Paris, da yarjejeniyar bakin haure ta duniya, da yarjejeniyar nukiliya ta Iran, da majalisar hakkin dan Adam ta MDD, da hukumar lafiya ta duniya da dai sauransu.

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

In dai mun yi nazari a kan dalilin ficewarta da komarta kuma, za mu gano cewa, kullum tana neman kujera a kungiyoyin duniya ne don biyan bukatunta, amma idan ba ta cimma buri ba sa ta fice. Lallai, don cimma moriyarta, da ma kiyaye babakeren da ta kafa ne take shiga kungiyoyin duniya.

Sai dai kuma neman wakilci a kungiyoyin duniya ba wasa ba ne, kuma bai kamata a mai da shi a matsayin dabarar yin takara da wasu don cimma burin siyasa ba.

Idan dai da sahihiyar zuci ne Amurka ke son komawa a wannan karo, to, ya kamata ta sauke nauyin da ke wuyanta, ta biya kudin karo-karo na hukumar yadda ya kamata, sa’an nan ta kiyaye cudanyar da ke tsakanin bangarori daban daban, da ma ikon mulki, da tsarinsu na mabanbantan kasashe, ta yi kokarin inganta fahimtar juna, da hadin gwiwa da tsakanin kasashe kambobin hukumar, don tinkarar kalubale na bai daya da duniyarmu ke fuskanta. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Gidan Yari Da Amurka Ta Kafa A Ketare Ya Keta Hakkin Bil Adama

Gidan Yari Da Amurka Ta Kafa A Ketare Ya Keta Hakkin Bil Adama

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.