Alhazan Nijeriya su 95,000 da suka gudanar da aikin hajjin bana, za a fara kwaso su zuwa gida Nijeriya a ranar 4 ga watan Yulin 2023.
Shugaban kwamitin Jiragen sama na hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Goni Sanda, ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki na aikin hajjin da aka gudanar a daren jiya Lahadi a Makkah.
- Bala Kauran Bauchi Ya Gwangwaje Alhazan Bauchi Da Kyautar Riyal Dari Uku-Uku
- Hajj 2023: NAHCON Ta Cancanci Yabo Da Jinjina Ba Kushe Ba – Almakura
Sanda, ya ce za a dawo da alhazan kamar yadda aka tsara jigilarsu zuwa kasa mai tsarki, inda ya kara da cewa, kowanne alhaji da jami’in aikin hajjin na hukumar ana sa ran za su yi kwanaki 40 a Makkah kafin a kwaso su zuwa Nijeriya.
A cewarsa, tun asali bisa al’ada alhazan da aka fara kai wa Makkah su ne wadanda za a fara kwaso wa zuwa gida Nijeriya, kuma wannan shi ne daidai da ka’idar Saudiyya.
Ya roki Alhazan da su nuna halin da’a a yayin da ake shirye -shiyen kwaso su zuwa Nijeriya daga Makkah.