Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya raba wa duk alhazan Jihar Bauchi riyal dari uku-uku bayan sun kammala sauke farali a birnin Makkah.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Mukhtar Gidado ya fitar a wannan Juma’ar, ta ce fiye da alhazan jihar 3000 ne suka samu wannan kyautar ta karin abin guzuri.
- Gwamnan Bauchi Ya Sake Nada Gidado A Matsayin Mashawarci Kan Yada Labarai
- Fitaccen Likitan Nan Dan Jihar Bauchi Farfesa Abdu Ya Rasu
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Alhaji Gidado na cewa gwamnan ya bayar da kyautar kudin ne ga alhazan jihar yayin da ya ziyarci sansaninsu a kasa mai tsarki.
Alhaji Gidado ya ce gwamnan wanda ya ziyarci sansanin alhazan a filin Mina, ya yaba da yadda suka zama jakadu nagari ta hanyar riko da kyawawan dabi’u da kiyaye dokokin kasar ta Saudiyya.
Kamfanin Dillancin Labaran na NAN ya ruwaito cewa kyautar riyal dari uku-uku da duk alhazan suka samu za ta iya kai Naira 75,000 a kudin Nijeriya.