Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya karbi bakuncin tawaga daga kamfanin raya man fetur na Shell a babban dakin taro na Aso Rock da ke Abuja.
Tawagar Shell a ziyarar ban girma karkashin jagorancin Daraktar kamfanin, Misis Zoe Yunovic tare da Peter Costello, Osagie Okunbo, da Mar De Jong.
- Tinubu Ya Yi Ganawarsa Ta Farko Da Hafsoshin Tsaro
- Hajjin Bana: Abin Da Ya Sa Alhazan Nijeriya 14 Suka Rasu
Babban jami’in rukunin kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC), Mele Kyari; da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila su ma sun halarci taron.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan makamashi, Olu Verheijen; mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga, Zacchaeus Adedeji; da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, ayyuka na musamman da dabaru, Dele Alake.
Taron na ranar Litinin ya biyo bayan komawar Tinubu Abuja a ranar Lahadi bayan da ya gudanar da bukukuwan Sallah a Legas a makon jiya.
A ranar 22 ga watan Yunin 2023 ne shugaban kasar ya yi ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Nijeriya a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Tinubu ya je birnin Paris na kasar Faransa, tare da shugabannin duniya irin su shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron domin taron sabuwar yarjejeniyar hada-hadar kudi ta duniya da aka gudanar a Palais Brongniart.
Bayan kammala taron na kwanaki biyu, shugaban ya zarce zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya domin yin wata ‘yar gajeriyar ziyarar sirri, sannan ya dawo Nijeriya domin gudanar da bukukuwan Sallah Babba a ranakun 28 da 29 ga watan Yunin 2023.
A zamansa na kwanaki biyar a Legas, Tinubu ya gana da sarakunan Yarbawa masu da suka hada da babban sarkin Ijebuland, Oba Sikiru Adetona; da Alake na Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun da sauransu.