Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Edo ta kama wasu dalibai biyu na Jami’ar Benin (UNIBEN), Samson Kennedy, dalibi mai mataki na 200 na nazarin kimiyyar kwayoyin halitta da Wilfred Emmanuel, dalibi mai matakin karatu na 500 a shahen nazarin idanu.
An kama su ne da laifin kai abokin aikinsu, mai shekaru 23, Francis Aniude (dalibi a sashen nazarin ilmin sinadarai) zuwa kogin Ekosodin, inda suka dulmiya shi a ciki.
- Sin Ta Bukaci Japan Da Kada Ta Yi Yunkurin Amfani Da Rahoton IAEA A Matsayin Izinin Zubar Da Dagwalon Ruwan Nukiliya A Cikin Teku
- Batun Sake Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Sikeli
Mutanen biyu, wadanda aka ce makwabta ne da Aniude, an yi zargin cewa sun gayyace shi zuwa kogin Ekosodin don yawon bude ido, inda ya suka dimiya shi a ciki.
An ce wadanda ake tsare da su din sun koma harabar jami’ar ne domin bayyana faruwar lamarin.
Wani dalibin daga sashen kimiyyar sinadarai da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “An dilmiya Francis ne a cikin kogin Ekosodin, a wata unguwar da ke kusa da makarantar a ranar 29 ga watan Yuni kuma aka ce ba a ganta ba. Wasu masu mutane da ked aura da abin ya faru suka tsinci gawarsa a ranar Asabar, 1 ga Yuli, 2023.
“Gano jini a lebansa da bawon igiya a wuyansa ya haifar da shakku tsakanin ‘yan uwa da dangi da suka nemi a yi musu gwajin gawar,” in ji shi.
Da yake tabbatar da rahoton, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce an kama mutanen biyu ne domin su taimaka wa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike kan lamarin.
“An dade ana kai karar a ofishin ‘yansanda na Ugbowo. Daga karshe jami’in ‘yansandan shiyya da mutanensa sun jagoranci tawagar ‘yan wasan ninkaya zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka yi sa’a, sun samu nasarar gano gawar.
An mayar da shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) don ci gaba da bincike. An kama mutane biyu, domin jin dalilin da ya sa suka tafi tare domin shiga wannan kogin a lokacin da wannan mummunan lamari ya faru.
“Kame su yana da matukar muhimmanci domin mu san abin da ya sa suka bar masaukinsu suka tafi wannan kogin da kuma jin ainihin abin da ya faru a kogin,” in ji shi.