A kwanan nan shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Jiangsu, wanda ke gabar tekun gabashin kasar Sin, inda ya ba da shawarar daukar Jiangsu a matsayin abin koyi, wajen gaggauta gina tsarin masana’antu na zamani, wanda zai dauki masana’antun kere-kere na zamani, da sassan tattalin arziki dake shafar kayayyaki na zahiri a matsayin kashin baya, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai inganci.
To ko wane irin tasiri gina tsarin masana’antu na zamani da Sin ke yi zai kawo wa tattalin arzikin duniya? Ko shakka babu, inganta aikin bude kofa ga kasashen waje mai inganci, ya kasance wani muhimmin bangare a tunanin Xi Jinping kan tattalin arziki. A yayin ziyarar da ya kammala, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara hada kan kasuwar cikin gida da ta ketare, domin samun ci gaba mai karfi da dorewa, kana za ta ci gaba da sabunta hanyoyi, da matakai na jawo jarin waje, da fadada bude kofa ga kasashen waje, don gina wata cibiya mai budaddiyar hanya biyu, dake iya hada kan duniya, da habaka bunkasuwar cinikayyar waje, ta hanyar yin kirkire-kirkire, kana da ci gaba da karfafawa, da fadada kasuwannin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)