Tsarin sadarwa ta fasahar GPRS (wato General Packet Radio Serbice) ita ce hanyar da ta kunshi aikawa da kuma karbar sakonnin da ba na sauti ko murya ba, tsakanin wayar salula da wata wayar ‘yar uwarta ko kuma kwamfuta.
Wadannan sakonni da ake iya aikawa ta hanyar GPRS dai sune rubutattun sakonnin tes (SMS) ko Imel ko mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ko kuma tsarin kira ta hanyar bidiyo ( bideo call) da dai sauransu. Wannan tsari na sadarwa na cikin sabbin tsare-tsaren da wayoyin salular da aka kera cikin zamani na biyu (2 Generation Phones) suke dauke dasu. Kuma ita ce hanya ta farko da ta fara bayyana wacce ke sawwake sadarwar da ta shafi rubutattun sakonni da na bidiyo da kuma mu’amala da fasahar Intanet.
- Abin Da Ya Sa A Daminar Da Ta Gabata Masara Ta Yi Tsada -Shugaba
- Gwamnatin Gombe Ta Sha Alwashin Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya
Amma kafin nan, tsoffin wayoyin salula na amfani ne da hanya kwaya daya wajen aikawa ko karbar dukkan nau’ukan sakonni. Idan kana magana da wani, to ko da an aiko maka rubutacciyar sako, baza ta shigo ba sai ka gama magana sannan ta iso. Idan kana son aikawa da rubutacciyar sako kuwa, ta hanyar aikawa da murya za ka aika, kuma da zarar ka fara aikawa, layin zai toshe, babu wanda zai iya samunka, sai lokacin da wayar ta gama aikawa, sannan za a iya samunka.
Wannan ya faru ne saboda wayoyin salula na zamanin farko (1 Generation Phones) na amfani ne da layin sadarwa guda daya tak. Wannan tsari shi ake kira Circuit Switched Data (CSD). Karkashin wannan tsari, kamfanin sadarwarka zai caje ka ne iya tsawon lokacin da sakonka ya dauka kafin ya isa, wanda kuma mafi karancin lokaci shi ne dakiku talatin (3o seconds).
To amma da tsarin sadarwa ta wayar iska na GSM ta bayyana, sai aka samu fasahar GPRS, wacce ke amfani da layin aikawa da karbar rubutattun sakonni kai tsaye tsakaninta da wata wayar ko kuma kwamfuta, idan ta Intanet ne. Hakan kuma na samuwa ne musamman idan wayar na dauke da fasahar ‘Wireless Application Protocol’, wato WAP, wacce ka’idar da ke tsara sadarwa a tsakanin kwamfuta da wayar salula, ta hanyar wayar iska. Karbar sakonnin tes ko Imel ko kuma mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar GPRS shi yafi sauki da kuma sauri wajen mu’amala. Sai dai kuma wannan tsari ta GPRS na cikin nau’ukan hanyar sadarwa da kamfanin sadarwa ne ke bayar dasu, wato Network Serbice.
Wannan ke nufin idan wayarka na da WAP, ko kuma tsarin mu’amala da fasahar Intanet, to kana iya amfani da ita kai tsaye wajen shiga Intanet. Kuma da zarar kayi haka, kamfanin sadarwarka zai caje ka kudin zama a kan layi. Tsarin sadarwa ta GPRS na amfani ne da wasu hanyoyi masu zaman kansu wajen aikawa da sakonni. Wannan tsari shi ake kira Multiple Access Method a Turance.