Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta saki Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma kuma tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari.
Sanata Yari wanda jami’an DSS suka tsare tare da yi masa tambayoyi, an sake shi a daren jiya da misalin karfe 11 na dare, kamar yadda majiyoyi suka ruwaito.
- Abin Da Ya Sa A Daminar Da Ta Gabata Masara Ta Yi Tsada -Shugaba
- Rusau: Kungiyoyi Sun Bukaci A Hana Gwamnan Kano Shiga Amurka
Idan za a tuna cewa Yari, wanda ya tsaya takarar shugaban majalisar dattawa, ya ziyarci ofishin hukumar tsaro ta farin kaya DSS a ranar Alhamis kuma an tsare shi.
Ba a san dalilin tsare Sanata Yari da yi masa tambayoyi ba.
Wani babban jami’in tsaro da kuma mai taimaka wa gidan gwamnatin jihar ya bayyana cewa hukumar DSS ta kama Yari a safiyar ranar Alhamis tare da tsare shi.
An tambaye shi dalilin da ya sa ya yi watsi da kiran wayar da shugaban kasa ya yi masa amma bai bada amsa ba.
Ya fara cece-kuce akan cewa yana da hakki na tsayawa takarar wannan mukami kuma yanke shawara kan harkokin siyasarsa.
“Shugaban yana kokarin rokonsa da ya janye aniyarsa ta ganin ba za a sake komawa irin zamanin Bukola Saraki lokacin da ya zama shugaban majalisar dattawa a 2015 ba.
“Duk mun san cewa bayyanar Saraki a wancan lokacin ita ce kuskure na farko da Shugaba Buhari ya yi, kuma hakan ya gurgunta shekarunsa hudu na farko a kan karagar mulki,” in ji majiyar.