Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani manomi mai suna Solomon Yusuf a lokacin da yake halartar wani daurin aure a unguwar Rakpami da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Sakataren kungiyar Gbagyi Cultural Renaissance Foundation a jihar, Musa Emmanuel-Dnasuwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lafia babban birnin jihar a ranar Lahadi.
- Ban Bada Umarnin Rufe Majami’ar Fadar Shugaban Kasa Ba —Remi Tinubu
- Gwamnan Kebbi Ya Kori Hadiminsa Kan Wallafa Wani Sako A Kafafen Sada Zumunta
Dnasuwa ya yi kira ga shugaban karamar hukumar Toto Aliyu Abdullahi-Tashas da Gwamna Abdullahi Sule da su hada kai da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu bayani kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp