Alkaluma daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, cinikin motoci a kasar Sin ya karu zuwa kaso 9.8 a kan na bara, inda adadin ya kai miliyan 13.24 a cikin rabin farko na bana.
Cikin watan Yuni kadai, an sayar da motocin da yawansu ya kai miliyan 2.62, wanda ya karu da kaso 4.8 a kan na makamancin lokacin a bara.
Kasuwar sayar da motoci ta kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri a rabin farko na bana, yayin da ake samun karuwar bukatarsu, inda aka samu ci gaba sosai a rubu’i na 2 na bana.
Kungiyar ta alakanta tagomashin da kyautata manufofin sayayya da rungumar tsauraran matakan rage fitar da hayaki mai guba da gabatar da wasu sabbin samfura da masu kera motoci suka yi da kuma karancin adadin da aka saya a watannin Afrilu da Mayu.
Alkaluman sun kuma nuna cewa, kasar Sin ta sayar da motoci masu amfani da sabon makamashi kusan miliyan 3.75 a rabin farko na bana, adadin da ya karu da kaso 44.1 a kan na bara, wanda ya kawo adadin irin motocin a kasar zuwa kaso 28.3. (Fa’iza)