Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya maye gurbin Ciyaman din kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Surajo Shuaibu Yahaya, da shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Hukumar Shirya Gasar Firimiya ta Kasa (LMC), ta dakatar tsohon Ciyaman din na Kano Pillars, Suraj Yahaya, wanda a ka fi sani da Jambul daga kungiyar.
- Musulman Kudu Maso Gabas Za Su Kaddamar Da Alkurāanin Da Aka Fassara Zuwa Harshen Igbo
- Masu Muguwar Niyya Ba Za Su Samu Biyan Bukata Ba
LMC ta ce dakatar Ciyaman din ta biyo bayan laifin cin zarafin mataimakin alkalin wasa da ya yi, yayin da Kano Pillars ta kara da kungiyar Dakkada FC a Kano.
A wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren yada labaran jihar, Abba Anwar, Ganduje ya ce “Kamar yadda kungiyar Kano Pillars ke kara fuskantar matsin lamba a gasar Firimiyar Nijeriya, zai yi kyau a samu shugabancin da zai jagoranci kungiyar.”
āIbrahim Galadima, shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, yanzu zai maye gurbin Ciyaman din Kano Pillars FC na yanzu, Surajo Shuāaibu Yahaya, a matsayin mukaddashi, kafin a nada Ciyaman na dindindin,ā cewar gwamnan.
Sanarwar ta ce nadin zai fara aiki nan take ne.