Sarakunan gargajiya, a karkashin Jagorancin kungiyar sarakunan wanzar da zaman lafiya, sun yi maraba da shirin majalisar wakilai don a ba su damar bayar da gudunmawa a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.Â
Idan ba a manta ba, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ne, ya shelanta cewa majalisar za ta yi aiki don tabbatar ta bai wa sarakunan damar bayar da gudunmawarsu a cikin kundin tsarin mulki.
- Dajarar Naira Ta Sake Faduwa Zuwa 803 Akan Kowace Dalar Amurka
- Da Dumi-Dumi: Farashin Man Fetur Ya Tashi Zuwa 617 Kan Kowace Lita
Ya bayyana hakan ne, a yayin ziyarar da ya kai fadar mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli.
A cikin sanarwar da Eze-Igwe William Ezugwu shugaban kungiyar na kasa, ya fitar a madadin sauran sarakunan, sun bayyana yunkurin majalisar a matsayin abin yabawa, inda suka ce sarakunan na da gudunmawar da za su iya bayarwa a kudin tsarin mulkin wajen wanzar da zaman lafiya da rage kalubalen rashin tsaro a kasar nan.
Kazalika, sun bayyana cewa yunkurin zai zama tamkar kafa tirihi ga majalisar ta 10, musamman don wanzar da zaman lafiya a fadin kasar nan.
Sun kara da cewa sarakunan kasar nan, sun jima suna fafutuka don a ba su dama bayar da tasu gudunmawar su a kundin tsarin mulkin kasar.
A cewarsu, sarakunan a shirye suke domin su bayar da shawararsu don tattauna kan maganar matukar an gayyace su.