‘Threads’ sabuwar manhaja ce (application) dangogin su Facebook, Instagram da Whatsapp. Manhajar Threads ta yi kama da Twitter sosai. Sai dai akwai abubuwa da suke da bambamci da Twitter.
A Twitter adadin harufa 280 ne za ka iya rubuta su, amma a Threads an ba ka damar rubuta harufa 500. A Twitter bidiyo mai tsawon dakika 20 ne za ka iya dora wa, amma a Threads za ka iya dora bidiyo mai tsawon minti biyar. A Twitter za ka iya yin tattaunawa da juna (chatting), amma a Threads a babu wannan damar.
Yadda ake yin rijista shi ne, za ka je ‘play store’ ko ‘app store’ ka sauke shi. Sai ka yi rijista. Amma dole sai kana da account da Instagram, sannan za ka samu damar yin rijista da Threads din.
Mutum miliyan goma ne suka yi rijista don amfani da sabuwar manhajar Thread a cikin sa’a bakwai da kaddamar da ita, in ji shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg.
Ya bayyana dandalin da cewa kishiya ce “da za ta yi zaman mutunci” da Twitter, wadda hamshakin mai arzikin nan Elon Musk ya saya a watan Oktoba.
Kwararru sun ce dandalin Threads zai iya jan hankalin masu amfani da Twitter wadanda ba sa farin ciki da sauye-sauyen da aka kawo wa manhajar a baya-bayan nan.
Threads na bai wa mai amfani da ita, damar wallafa haruffa sama da 500, kuma tana da siffofi irin na Tuwita.
Tun farko, Mista Zuckerberg ya ce gudanar da dandalin “mai saukin kai ga masu amfani… zai kasance muhimmin lamari wajen samun nasarar manhajar”.
Sai dai Mista Elon Musk ya mayar da martanin cewa: “Tabbas ya fi sauki, wasu bakin ido su far maka a Tuwita, da mutum ya buge da karyar samun farin ciki daga Instagram na boye.”
Katafaren kamfanin Meta wanda ya mallaki shafin Facebook da Instagram ne, ya kaddamar da manhajar sada zumunta da muhawarar, mai suna Threads, da galibi ake kallo a matsayin kishiya ga Twitter.
Ba ma ga kwararrun da ke kallon kaddamar da sabuwar manhajar ta Threads a matsayin kishiya ga Twitter mallakar Elon Musk ba, Mark Zuckerberg da kansa ya furta cewa Threads wanda ya kunshi abubuwa kusan irin na Twitter zai iya yi wa Tuwita fintinkau.
Duk da yake, zuwa yanzu ba a kaddamar da sabuwar manhajar sada zumunta da muhawarar a yankin Tarayyar Turai ba, amma Mista Zuckerberg ya ce a cikin sa’a hudu da kaddamar da shi har ya samu masu amfani da shi sama da miliyan biyar.
Ya kara da cewa zai dauki lokaci kafin sabon dandalin ya buwaya, amma dai mai yiwuwa ne Threads ya samu yawan mutane sama da miliyan dubu daya.
A cewar Zuckerberg, Twitter ya samu wannan damar, sai dai bai yi amfani da ita ba. Amma ya ce su suna fatan za su yi.
Sai dai abokan gogayya sun yi suka a kan yawan bayanan masu amfani da ita da manhajar za ta rika tattarawa.
A ciki akwai batun lafiya da na kudi da kuma bayanan mai shiga shafin , in ji rumbun Apple Store.
A yanzu dai ana iya sauke wannan manhaja ta sabon shafin na sada zumunta da muhawara na Threads, a sama da kasashe 100, ciki har da Birtaniya, amma ban da kasashen Tarayyar Turai.
Kamfanin Meta da ya mallaki wannan sabuwar manhaja ya ce, a yanzu zubin farko ce, wanda hakan ke nufin akwai karin wasu abubuwa da ya shirya sanya wa manhajar domin kara jan hankalin jama’a
Kasancewar shafin na da alaka da Instagram wanda ke da tarin mabiya, wannan zai sa ya samu saukin daukar hankalin tarin miliyoyin mabiya da ke kan Instagram, wadanda tuni wasu ma har sun dade da sauke shi.