Sana’ar gyaran gashi sana’a ce wacce ake yin ta ta hanyar gyara gashi na mata kamar wanke gashi, stretching wato mike gashi ko kuma steaming gashi har da ma kitsa gashin.
Gyaran gashi abu ne wanda ke matukar kawata mace a kowane irin zamani ne na al’umma a duniya. Sana’a ce wacce mace za ta iya yinta a gida ko kuma ta bude shago ta yi kuma tana da dimbin riba domin mace dai an san ta da gyara kuma kusan kashi 80 na mata sun fi zuwa inda za a gyara musu kai da kan wankewa a gida za ka iya zuwa saloon idan ka na gaggawa.
Abubuwan bukata yayin fara wannan sana’a su ne:
Hair stretcher, hair dryer, kujeru na zama drawer comb, man gashi rollers. Shampoo, na’urar turara gashi
Amfanin kayayyakin da na lissafa a sama su ne:
Shampoo: wannan shi ne ake amfani da shi wurin wanke gashi, idan aka wanke gashi da shampoo sai a saka conditioner a kan don ya kare karyewar gashi, Stretcher (na’urar mikar da gashi): wannan wata na’ura ce da ke amfani da wuta ne karama wanda ake amfani da ita wurin mikar da gashi bayan an wanke gashi sai a busar da tawul da kuma hand drier sai a jona na’urar da wutar lantarki za ta yi zafi sai a rika yankar sumar kadan-kadan a na saka na’urar mikarwar har a gama.
2. Hair dryer (na’urar busar da gashi): wannan na’ura ne na busar da gashi.
3.kujeru: wadannan kujeru su ake amfani da su gun zama: Kwastomominka za su zauna a kai
Madubi: Ya kamata mai wannan sana’a ya kasance yana da madubi babba don kwastomominsa su gani.
Rolas na gashi: Wannan ana amfani da shi wajen nade gashi kafin a shiga ‘dryer’ wato na’urar busar da gashi.
Drawer: Wannan shi ne inda za’a saka kayayyaki kamar su man kitso, man relader da sauran su.
Na’urar turara gashi: Na’ura ce da ke turara gashi kuma treatment ne da ke kara tsawon gashi idan an bi shi da ka’ida.
Man gashi: Mayuyyuka ne na gyaran gashi wadanda idan an wanke an gyara a ke shafawa, za ka iya kawata shagonka duk yadda ka ga dama, iya kudin ka iya shagalin ka har kitso ma ana yi a saloon.
Sana’a ce mai riba sosai kuma ba ta bukatar jari mai yawa, sannan ana samun kwastomomi sosai musamman lokacin Sallah.
Idan ka iya yin lalle nan ma wata karin riba ce sosai, ana gyaran farce ma a saloon na kafa da na hannu.a na kuma make up ya danganta da yanayin jarinka da kuma kwarewarka. Allah ya ba da sa a.