Mai shari’a Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke Legas, ya bayar da belin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele a kan kudi naira miliyan 20.
Ana tuhumar Emefiele bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da mallakar bindiga da harsasai 123 ba tare da lasisi ba.
- An Gurfanar Da Emefiele A Kotu Kan Mallakar Makamai Ba Bisa Ka’ida Ba
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Boko Haram Kan Zargin Shirin Kai Hari Gidan Atiku
Sai dai Emefiele ya musanta zargin da ake masa.
Bayan karar da ya shigar, lauyan wanda ake kara, Mista Joseph Daudu, SAN, wanda ya jagoranci wasu manyan lauyoyi hudu, ya sanar da kotun bukatar neman belin wanda ake karewa.
Lauya Dedence ya shaida wa kotun cewa an tsare wanda ake tuhumar ba bisa ka’ida ba.
Sai dai mai gabatar da kara, Misis N.B Jones, ta ki amincewa da neman bayar belin Emefiele kan hujjar cewa ba a ba ta kwafin takardar bukatar belin nasa ba.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Oweibo ya amince da bukatar lauyoyin kan hujjar cewa laifin da ake tuhumar ake yi wa Emefiele bai cancanci a tsare shi na tsawon wannan lokaci ba.
Kotun ta ce ba za a hana belinsa ba duba da sashe na 162 na kundin dokar laifuka.
Saboda haka, kotun ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira miliyan 20 tare da gabatar da mutum daya da zai tsaya masa.
Kotun ta yanke hukuncin cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya bayar da wata takardar shaida kuma ya kasance yana da adadin kudin da aka bayar da belin a kasa.
Ya bukaci da a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan yari har sai an cika sharudan belin.
Kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.
Tun da fari, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Laifin da ta ce ya ci karo da tanadin sashe na 4 da 8 na dokar mallakar mallamai na 2004.