Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da cewa kuri’un ‘yan Nijeriya ne kadai zai tabbar da wanda ya yi nasarar lashe zabe a 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya tabbatar da hakan lokacin da yake tarbar tawagar wakilan Majalisar Dinkin Duniya a Abuja.
Ya kara da cewa hukumar zabe za ta yi duk abin da ya dace wajen ganin babban zabe a Nijeriya ya ci gaba da karbuwa a idon duniya.
Ya ce, “Nina mai tabbatar muku cewa za mu ci gaba da duk abubuwan da suka dace da doka wajen ganin ‘yan Nijeriya sun zabi shugabanninsu ta hanyar da ya kamata.
“Kuri’un ’yan Nijeriya ne kadai zai tabbatar da wanda ya samu nasarar lashe zabe a 2023, sannan kuma za mu ci gaba da mutunta zaben ‘yan Nijeriya.
“Ina mai tabbatar muku cewa ba za mu taba rintsawa ba har sai mun tabbatar an gudanar da sahihin zabe a Nijeriya ta yadda dimokuradiyya za ta zauna da kafarta. Mun ji dadin kasancewa da ku kuma muna sa ran za su gan ku lokacin gudanar da babban zabe a 2023,” in ji shi.
Farfesa Yakubu ya ci gaba da cewa hukumarsa za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen huda da ‘yan jarida da jami’an tsaro da kawayenta na kasa da kasa kamar irin su UNOWAS.
“A duk lokacin da muka zo kan wannan manufar, muna samu gwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da abubuwa yadda ya dace, akwai abun da muke bukata shi ne zaman lafiya da lumana a yankunamu.”
Farfaesa Yakubu ya gode wa UNOWAS bisa a ko da yaushe take turo tawaga wadanda za su saka ido a lokacin gudanar da zabe a Nijeriya.
Da yake gabatar da jawabi, wakili na musamman ga Sakataren Majalisan Dinkin Duniya kuma shugaban UNOWAS a yankin Yammacin Afirka, Mahamat Saleh, ya bayyana cewa zaman lafiya da lumana a Nijeriya shi ne babban burinsu.
Ya ce, “Mun zo Nijeriya ne a wannan lokaci bisa shirye-shiryen babban zabe a 2023. A wurinmu zaman lafiya da lumana da tsaro a Nijeriya shi ne babban burinmu. A ko da yaushe ina matukar yin misali da Nijeriya, muna murna ganin yadda aka zabi ‘yan takara.
“Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da goyon bayan Nijeriya domin ganin an gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana. Muna taya ka murna kuma za mu goyi bayanka kan ayyukan da ka gudanarwa da wadanda kake kokarin yi a wannan zabe mai zuwa,” in ji shi.