Fitacciyar matashiyar marubuciyar littafan Adabin Hausa da ke cin kasuwarsu a intanet, wato ZAINAB SALIHU YARIMA da aka fi sani da ‘Sarauniyar Kanawa’ ta yi kira ga takwarorinta marubuta da su ji tsoron Allah su zama masu tsaftace alkalumansu, don rubuta abun da zai zama mai amfanarwa ga al’umma baki daya, wanda bai ci karo da addini da kuma al’adar Malam Bahaushe ba. Har ila yau marubuciya Zainab ta yi wasu bayanan na daban game da rubutu a wannan zamanin, a yayin tattaunawarta da wakilinmu ADAMU YUSUF INDABO. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta Kasance:
Wace ce Zeey Sarauniyar Kanawa?
To da farko dai sunana Zainab Salihu Yarima, wacce aka fi sani a media da duniyar rubutu kuma shi ne Zeey yar mutan Zazzau, ko Sarauniyar Kanawa. An haife ni a garin Zaria, na yi makarantan primary na a Saminaka da islamiya daga baya na dawo Zaria na yi secondry school dina, sannan na tafi Makarfi na yi school of health, yanzu haka ina aiki a ‘Barau Dikko Teaching Hospital Kaduna.’ Takaitaccen tarihina ke nan. Amma shi lakabina na ‘Sarauniyar Kanawa’ ya samo asali ne daga zauren ‘Majalisan Marubuta’ irin ana chat din nan, kanawa kowa ya taso mun suna tsokana ta ina ramawa, ga shi ni kadai ce a lokacin bazazzagiya, sai na ce musu su bi ni a hankali fa, domin ni sarauniyar su ce. Aka dunga musu na ce ni daga yau ma sunana sarauniyar kanawa. Ai sai ma na canja group name dina zuwa Sarauniyar Kanawa. To tin daga wannan lokacun sunan ya bi ni.
To ta ya Zeey ta tsinci kanta tsamo-tsamo a duniyar rubutu?
To a gaskiya dai ni na kasance ma’abociyar karance karance tun ina primary school da na fara iya hausa nake karatun littafi irin su magana jari ce, iliya dan mai karfi, Shehu umar da dai sauran su, to bayan na shiga secondry school dina sai na koma karatun littafan yaki har ta kai ta kawo ina samun littafi ina rubutawa. Idan na rubuta in zauna ina karanta ma kawayena haka in an fita break su yi ta yabawa suna fadin ya yi dadi ni kuma in ta jin dadi da kara samun kwarin gwiwa. To tun daga lokacin na fara rubuce rubuce har ranar da na san ana rubutawa ta waya, ni ma kawai sai na bi sahu, shi ne har yau ake damawa da ni.
Tun wacce shekara kika fara rubutun ke nan?
Eh to shekarar da na fara rubutu a media zan iya tunawa a shekara ta 2019 ne na fara littafina a media. Amma asalin fara rubutuna na littafi tun a makaranta ne, lokacin ina aji biyu na sakandire a shekara ta 2008.
To wanne littafi ne farko da kika fara rubutawa?
Gaskiya wadancan da na rubuta a makarantar ba suna, kawai labarin nake rubutawa kara zube. Amma littafinna na farko a media shi ne GIDAN GADO.
Su wadancan na makarantar daga daya ba ki sabunta su kin musu suna ba?
Gaskiya ban musu ba, saboda littafan da na yi rubutun ma a cikin su duk sun bace. Amma lokacin dai ina yin rubutun ne irin labaran yaki din nan, domin ni masoyiyar littafan Abdulazeez sani madakin gini ce, a da ba wani sabon littafin shi da zai fito ban karanta ba. Saboda kaf cikin marubuta shi ne gwanina.
To yanzu daga fara rubutun ki zuwa yau, kin rubuta littafi guda nawa?
Na rubuta littafai guda bakwai su ne: Gidan Gado, Wa Zan Aura? Sanadin Abayar Sallah, Boyayiyar Kulli, Gwaji Kafin Aure, Kisan Rudu, da kuma Baitul Jinn.
Kin ce littafinki na farko a media shi ne Gidan Gado, to shi me ya kunsa?
To shi littafin Gidan Gado na yi shi ne a kan yanayin rayuwa irin ta gidan yawa dnn nan, gidan gado gidaje irin namu na iyaye da kakanni wato Gidan Gandu. To akwai wata yarinya da ta taso a cikin gidan, tana da farin jini da sauran su haka. Sai wasu daga cikin dangi a gidan suka sa ta a gaba da hassada da dai sauran su, amma daga karshe kuma ita ce ta zama ma dangin nasu fitala. Saboda dama masu iya magana sukan ce hassada ga mai rabo taki ce. Kuma sara da sassaka ba ya hana gamji tofo.
Kuma cikin wadannan littafai guda Bakwai da kika yi, wanne ne bakandamiyarki a cikin su?
‘Kisan Rudu’ saboda shi littafin kisan rudu tsantsan cakwakiya ce da cin amana da rikita rikita. Labari ne a kan wata yarinya da kakarta, inda yarinyar ta kai karar kakarta a kan cewa ita ta kashe mata mahaifiya, a gefe guda kuma kakar ta taka sahun barawo, in da ya kasance kullum kirarin kakar ke nan a kan cewa ita ce ajalin sirikar tata, da wannan daman aka hada baki da ‘yar aka kashe uwar sannan aka makala wa kakar cewa ita ta kashe uwar. Don haka aka dunga tafka shari’a, an dauki tsawon lokaci ana shari’a, sai daga karshe kwatsam aka gano uwar bata mutu ba, sai ga ta ta bayyana a gaban kotu. Gaskiya ina son labarin nan domin labari ne da ya dauki hankali masu karatu sosai, domin labari ne mai cike da sarkakiya ba za ka taba fahimta labarin ba sai ka kai karshen labarin. Shi ya sa labarin ya samu karbuwa sosai.
To cikinsu kuma wane ya fi ba ki wahala wajen rubutunsa?
‘Baitul Jinn’ littafin na daya ne da na biyu. Na farkon free ne na biyun kuma na kudi. Shi ya ke kan wahalar da ni domin ina saka zaren labarin ne yana neman kufce mun. Labari ne da ya kunshi aljanu da mutane, sannan ya ke nuni ga mutane masu sakaci da ibada, ba su damu da neman ilimi a kan addini ba sai na zamani kawai da rayuwar zamani. To labarin ne na da tsayi ina shan wahala sosai wajen yin typing, ga shi na karbi kudin mutane na kasa karisa musu, ko na ce zan takaita shi ba zan iya ba. Ga shi mutane suna matukar son labarin, kullum na hau media sai an tambaye ni yaushe zan kammala Baittul jinn part two domin wasu sun ce sai ya yi complete za su siya. Gaskiya labarin ya ja hankali mutane sosai. Ga labarin ya ki bari na sukuni ban kuma iya typing labarin da Asuba kamar yadda nake sauran labaraina sai da daddare kaman irin sha biyun daren nan duk da labari ne mai cike da abubuwan tsoro ni kaina wata ran ina jin tsoro in ina rubuta labarin.
Ke nan da asubah kika fi jin dadin yin typing sai kuma tsakar dare?
Eh gaskiya na fi jin dadin typing da Asuba, in kuma ina Asibiti ne ina aikin dare to na fi jin dadin typing a lokacin don ya na deben kewa ya hana ni jin barci. Gaskiya ni a kowanne yanayi ina iya yin typing, lokacin da ina cikin bacin rai da damuwa, da kuma cikin farin ciki da walwala duk ina iya yin rubutu.
To kuma ya batun kungiyoyin marubuta?
Eh ina cikin kungiyar Arewa writters, sannan ina cikin kungiyar Marubutan jahar Kaduna.
To daga fara rubutun ki zuwa yau wacce nasara kika cimma ta fuskar rubutu?
Gaskiya nasarorin da na samu ta fannin rubutu ba zai kidayu ba, kadan daga ciki dai shi ne na hadu da mutane kala-kala wanda ban taba tunani ko mafarkin haduwa da su ba, sai ga shi na hadu da su har mun zauna inuwa daya duk ta sanadin rubutu. Sai wani kyauta da aka taba min sanadin rubutuna na kisan Rudu, ina zaune kwatsam aka kira ni aka ce in zo tasha in karbi wani sako na ce sakon me ke nan aka ce dai in je in karba bayan na karbo sakon na bude na yi matukar farin ciki domin sako ne da ban taba zata ko tunanin samun shi ba a lokacin kuma duk ta sanadin rubutu.
To Ya batun kalubale?
Eh to ka san a komai bawa yake yi sai ya fuskanci kalubale amma ni gaskiya ban wani fuskanci kalubale game da fara rubutuna a gida ba ko cikin dangi. Kawai dai sai dan kalubalen da ba a rasa ba na masu karatu wanda za ka ga wata in ta fada ma wani magana tamkar ka bar yin rubutu. Domin na sha fuskantar hakan daga makaranta. Wasu makarantan su ne ciwon kan marubuci.
Wanne kira za ki yi ga yan uwanki marubuta?
Tom kiran da zan yi ga ‘yan uwana marubuta shi ne mu ji tsoron Allah mu san cewa marubuta tamkar madubi muke ga al’ummah domin duk abun da muka rubuta a littafanmu yana zamantowa wasu daga cikin al’ummah abun koyi ko abun kallo, saboda haka mu tsaftace alkalaminmu mu rubuta abubuwa masu muhimmanci wanda ko bayan ranmu zai amfani al’umma baki daya. Daga karshe kuma zan ce Allah ya kara hada kan marubuta, ya kara mana basira da daukaka baki daya.
To wanne sako kike da shi ga masoyanki, sannan wacce hanya za ki ba su na haduwa da ke don kulla zumunci?
Sakon da zan bayar ga masoyana shi ne ni ma ina matukar kaunar su a duk in da suke, sannan Sarauniyar kanawa mutun ce mai matukar saukin kai, da son duk wanda yake kaunar ta. Kuma duk wani mai son gani na ko haduwa da ni kofa a bude take ni mutuniyar Zazzau ce birnin shehu aljannar kanawa, amma mazauniya kaduna.
To Hajiya Zainab mun gode.
Ni ce da godiya.